Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Shiekh Lawan Hassan Abubakar
An haifi Sheikh Lawan Hassan Abubakar a garin Liman Katagum a Jihar Bauchi da ke Najeriya. Ya soma karatu ne a wajen ɗan uwan mahaifinsa Malam Ɗan Umma inda daga baya kuma ya yi karatu a wajen Malam Mahmud Tapare da kuma Malam Manu.
A wajen waɗannan malaman uku ya yi karatun Al-Ƙur'ani inda daga baya ya koma garin Bauchi ya yi karatu a nan.
A Bauchi, Malam ya yi karatu a wajen Malamai da dama kuma daga cikinsu akwai Malam Idris Kawu Mai Rubutu inda ya yi karatun littafin Malikiyya a wajensa har ya kai Risala.
Bayansa kuma ya yi karatu a wajen Malam Adamu da ke Unguwar Makama wanda mutumin Zaria ne inda ya yi karatu sosai a wajensa.
A 1992 ne malam ya shiga makarantar koyon ilimin Addinin Musulunci ta Bauchi.
Bayan Malam ya kammala makarantar, ya yi ta ƙoƙarin zuwa ƙasar waje inda ya ce wasu daga cikin abokan karatunsa sun samu nasarar amma shi ya tsaya a Najeriya inda ya ci gaba da bin malamai zaure domin samun karatu.
Haka kuma Malam ya samu yin karatu a cikin garin Abuja da garin Keffi da Nasarawa.
Sheikh Lawan Hassan ya yi karatu a wurin Malam Mukhtar Lawan a garin Abuja inda ya samu karatu a wajensa bayan ya dawo daga Madina haka kuma ya yi karatu a wurin aminin Malamin mai suna Malam Yusuf Goronyo wanda masani ne a ɓangaren Fiƙihun Malikiyya da Arabia da Nahawu.
Bayan nan ya koma Keffi inda ya koma wurin Malam Yahaya Mai Tabarma inda ya shafe kusan shekara biyar. Bayan rasuwar Malam Yahaya, akwai babban ɗalibinsa na Unguwar Yarabawa a Keffi inda ya ɗora da karantar da shi.
Akwai kuma Sardaunan Malamai a Maraba kuma ya yi karatun Lugha a wajensa da kuma Fiƙihu na Malikyya.
Yawancin karatun da ya yi ya yi shi ne ta hanyar bin malamai zuwa gidajensu ko kuma zauruka inda ya ce bai zauna aji ya yi karatu sosai ba a makaranta.
Abin da Sheikh Lawan ya fi ƙwarewa shi ne ɓangaren shari'a da kuma litattafai na Fiƙuhu musamman ma na Malikiyya.
Surar da ta fi ba malam wahala wajen hadda
Malam ya bayyana cewa surar da ya sha matuƙar wahala a wajen haddace ta ita ce Suratul Mutaffifeen.
Malam ya bayyana cewa ya sha duka ƙwarai dagaske kafin ya iya surar. Haka kuma ya bayyana cewa Suratul Inshiqaq ta ba shi wahala kafin ya iya karantata a gaban malam.
Surar da malam ya fi so
Malam ya bayyana cewa yana son surorin Al-Ƙur'ani matuƙa amma surar da ya fi so da jin daɗin karantata ita ce Suratul Kahf.
Malam ya ce duk lokacin da ya karanta surar ko da yana cikin damuwa ne yakan ji damuwar ta tafi
Tambayoyin da aka fi yi wa malam
A cewar Sheikh Lawan, an fi yi masa tambaya kan mu'amala ta yau da kullum da ta shafi mu'amalar aure da ta tsakanin mutum da mutum.
Malam ya ce duk da yake ana tambayar abin da ya shafi ibada, amma an fi yi masa tambaya a kan mu'amala.