Me ya sa wasu 'yan Najeriya ke sayen ƙaramin ƙunshin audugar mata?

    • Marubuci, Olivia Ndubuisi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Abu ne mai wuyar gaske ga kowace mace a duniya ta iya kammala kwanakin hailarta da audugar mata biyu kacal.

Hatta fakitin audugar mai guda takwas ba lallai ya isa ba, amma a Najeriya ana sayar da ƙunshi ko kuma audugar leda a matsayin audugar mata mafi sauƙin kuɗi da mutane za su iya saya.

A manyan ƙasashe masu arziki, ana ganin ƙunshin a matsayin isasshe kuma abin a dogara da shi, amma a Najeriya ana kallonsa a matsayin abin damuwa.

Fitowar audugar cikin irin waɗannan ƙaramin ƙunshi "abin damuwa" ne, in ji wata likitar mata mai suna Dr Chioma Nwakanma.

Amfani da su ba ya kawo sauƙi, hasali ma ya fi wahala saboda wasu matan ba sa iya kammala kwanakin haila da su.

"Ko da a ce ma ƙunshin na mai ƙwara takwas ne ba sa isa, saboda haka yanzu mutane na sayen fakitin sai su dinga zaɓar ranar da za su yi amfani da ita," kamar yadda Dr Nwakanma ta faɗa wa BBC.

"Zaɓin abin da za a yi amfani da shi a madadin audugar - tolifefa da tsimma - ba su da tsafta kuma suna da haɗari, saboda haka abin da ke faruwa ba zai musaltu ba."

Ɓullar irin waɗannan ƙunshi na kayayyaki masu muhimmanci da kuma kayan abinci na kwali na bayyana yanayin rayuwa da ake ciki ƙarara a Najeriya.

Yayin da hauhawar farashi a watan Maris na 2021 ya kai kashi 18 cikin 100 sannan farashin kaya ya kai kashi 23, tsadar rayua da hauhawar ta haifar ta sa wasu na cewa an samu "tattalin arziki na ƙunshi".

Ba audugar mata kaɗai ba, har da kayan abincin yara da man girki da kayan karin kumallo ana sayen su ne a ƙananan mazubi, wanda ta hakan ne kaɗai ake iya saya saboda farashinsu ya zarta samun mutane da dama.

"A da katan-katan na abubuwa nake saya saboda sun fi daɗewa. Yanzu kuwa mazubin da na samu mafi arha nake saya." in ji Chika Adetoye, wadda ta nuna damuwa kan yadda take ciyar da yaranta uku.

An fara lura da sayar da abubuwa a ƙaramin mazubi ne a ƙarshen 2020 yayin da aka fara yaɗa hotuna a shafukan zumunta na abubuwan da mutane ke cewa ba su taɓa ganin su a ƙananan mazubi ba, ciki har da giyar leda.

Kasuwar Oyingbo da ke Legas na cikin wuraren da ake tafka ciniki tsakanin mai saye da mai sayarwa, amma yanzu da kyar ake samun ragi.

"Abubuwa sun yi tsada yanzu, mutane ba sa iya saya," a cewar wata mai shago Nancy Ike.

Wata alama da ke ƙara fito da tashin farashi ita ce, a yanzu mutane kan sayi doya guda ɗaya jal maimakon a da da suke sayen kashi guda.

Gloria Joseph-Raji, wata masaniyar tattalin arziki da ke aiki da Bankin Duniya a Najeriya, ta alaƙanta lamarin da manufofin gwamnati.

A 2015 ne Babban Bankin Ƙasa na CBN ya lissafa abu 41 ciki har da shinkafa da bota (da ake cin burodi) da tumatur - har ma da jirage na ɗaiɗaikun mutane - cewa suna cikin kayayyakin da ba za a ƙara bai wa masu kasuwancinsu tallafin kuɗin ƙasar waje ba.

An ɗauki matakin ne saboda a rage yawan shigo da kayan daga ƙasar waje da kuma ƙarfafa gwiwar samar da su a cikin Najeriya. Tun daga lokacin ne kuma gwamnati ta dinga ƙara yawan kayayyakin, inda aka saka sikari da alkama a watan Afrilun 2021.

A ƙarshe ma har sai da gwamnati ta rufe iyakokin ƙasar a 2019.

"Waɗannan hauhwar da muke gani a yanzu, sun fara ne tun 2019 jim kaɗan bayan rufe iyakokin," a cewar Ms Joseph-Raji.