Ga dalilin da ya sa muka zo zamanin da ake kirkirar tsibirai

An aerial view of the Palm Jumeirah island in Dubai, UAE

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

A tarihi dan adam ya nemi yadda zai samar da busasshen fili daga tekuna domin mayar da shi gari wanda mutane za su iya zama a ciki.

Amma zamanin yanzu ya kawo wani sabon salo. A yanzu, muna ganin yadda ake ta samun tsibirai a cewar masanin kimiyyar kasa, Alastair Bonnett daga Jami'ar Newcastle da ke Birtaniya.

"Ana ta gina tsibirai yadda ba a taba yi ba a baya."

Wannan sabon zamanin na tsibirai ne da suka fi girma da kuma tasiri fiye da yadda magabatanmu suka tsara tsibiriai a baya, a cewar Bonnett a cikin litafinsa mai suna Elsewhere: A Journey Into Our Age Of Islands.

Masanin ya ziyarci tsibirai wadanda mutane suka gina da kansu a duk fadin duniya, inda ya sanya ido kan yadda aka gina su.

Manyan gine-gine wadanda aka yi ta hanyar zuba miliyoyin tan na kasa a cikin teku. Da wasu gine-ginen masu karfi wadanda ke iya rike karfin soji da duk abin da ya shafi yakin siyasa.

Akwai kuma karafunan mai wadanda suka shiga cikin kasa.

Yayin da wasu gine-gine suka lalace sakamakon sauyin yanayi, yin sababbi zai dauki laokci. Yawanci ba a cika samun abubuwa masu rai ba a kasan tsibiran da dan adam ya gina.

"Tsibiran da dan adam ya gina ba su cika samun abubuwa masu rai a kasansa ba, samun hakan abu mai wuya ne,'' in ji Bonnett.

A wurare kamar Tekun Kudancin China, "abubuwa da suke da daraja a da, an hallaka su saboda wadannan gine-gine."

Amma duk da haka, Bonnett ya tsinci kansa yana ganin sha'awar wadannan abubuwan, domin ya gano yadda aka gina su da kuma me yasa aka yi su.

Ko kana sonsu ko ba ka sonsu, za su gayawa mutane yadda duniya take a zamainin da.

An aerial view of The World islands in Dubai, UAE

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kirkiri taswirar Dubai mai kama da duniya ne saboda masu arziki, amma har yanzu mafi yawan tsibiran kasa ne, yayin da sauran kuma aka ware su don gina otel-otel da gidaje
A dredger pumps sand onto an artificial island in Dubai, UAE

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani jirgin ruwa a yankin Mashigin Gulf na tona himilin yashi wanda za a rufe ruwa da shi don samar da tsibiri
A view of the artificial island known as The Pearl off the shore of Doha, Qatar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan hadadden tsibitin na Pearl a Qatar girmansa ya kai kusan murabba'in kilomita hudu kuma an kashe biliyoyi wajen samar da shi
Swan Island in Paris photographed from the Eiffel Tower

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An samar da Tsibirin Swan a Paris a farkon shekarun 1800 don ya zama kariya ga gadojin birnin
An aerial view of Venetian Islands off the coast of Miami in Florida, US

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amma a farkon karni na 20 an sayar da gidajen da ke kan tsibirai shida na Tsibiran VEnetia a yayin da har yanzu wasu ke karkashin ruwa
A satellite image of the Palm Island and Hibiscus Island in Miami Beach, Florida, US

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An tsara tsibiran Venetia don su fi kowanne girma, amma mahaukaciyar guguwa da ta faru ta lalata tsarin
An aerial view of the Palm Jumeriah island in Dubai, UAE

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tsibirin Palm na Dubai na bukatar tan miliyan 120 na yashi don gina shi
A scenic view of Balboa Island in Southern California, US

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gina Tsibirin Balboa a California amma mazauna wajen na fama da rashin ababen more rayuwa tsawon shekaru
A satellite image of the Balboa Island, Newport Beach, California, US

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A yanzu Tsibirin Balboa na daga cikin mafi tsada a Amurka, inda mutum 3,000 ke zaune a can
Aerial image of two offshore oil platforms, Cromarty Firth, Scotland, United Kingdom

Asalin hoton, Getty Images

Oil rigs off the coast of Invergordon in Scotland

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Oil rigs can appear like alien structures from afar
A satellite image of Subi Reef, an artificial island being developed in the South China Sea.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ga wani Tsibirin ma na Subi Reef a kudancin tekun China
A view of the Qingdong-5 artificial island off the shore of Dongying in east China's Shandong province.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, China wajen samun man fetur