Kazakhstan: Sojojin Rasha sun shiga ƙasar domin mayar da doka da oda

An wallafa

Wata rundunar sojojin Rasha sun sauka a Kazakstan bayan da shugaban ƙasar mai mulkin kama karya ya bukaci haka, yayin da tashin hankali da tarzomar ƙin jinin gwamnati suka mamye manyan biranen ƙasar.

An ji karar bindigogi masu sarrafa kansu cikin babban birnin ƙasar Almaty bayan da tashin hankali ya ɓarke na kwanaki masu yawa saboda ƙarin kaɗin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

Jami'an gwamnati sun sanar da cewa fararen hula da 'yan sanda sun rasa rayukansu.

Sai dai shugaban kasar ya ɗora alhakin rikicin kan waɗanda ya kira "ƴan ta'adda", amma bai bayar da wata hujja ba.

Yayin wani jawabi da yayi a tashar talabijin mallakin hukumomin kasar, Shugaba Kassyn-Jomart Tokayev ya roƙi kungiyar tsaro ta CSTO wadda Rasha ke jagoranta, ta taimaka ma sa kwantar da tarzomar. Rasha da Kazakhstan da Belarus da Tajiskistan da Armenia ne mabobin wannan kungiya.

An kiyasta sojojin da Rasha ta aika sun kai 2,500.

Wani rahoto ya ce an kashe jami'an tsaron Kazakhstan 18 a Almaty, amma ƴan sandan ƙasar sun ce sun kashe gomman fararen hula da suka kira "masu tazoma".

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Kazakhstan ta sanar cewa an kama masu zanga-zanga 2.298.

Ranar Lahadi ne dai tashin hankali ya barke bayan da aka ninka farashin man LPG da yawancin ƴan Kazakhstan ke amfani da shi a motocinsu na hawa - lamarin da ya haifar da zanga-zanga nan take.

Gwamanatin kasar ta yi alkawarin janye ƙarin har sai bayan wata shida mai zuwa, amma alkawarin bai kwantar da hankalin ƴan kasar ba.

Taƙaitaccen bayani kan ƙasar Kazakhstan

A ina ta ke? Kazakhstan na maƙwabtaka da Rasha a arewa, da kuma China a gabas. Ƙasa ce mai fadin kasa, wadda girmanta ya kai na dukkan ƙasashen yammacin Turai.

Me yasa ta ke da muhimmanci? Ƙasar na da dumbin albarkatun ƙarkashin ƙasa, inda kashi 3 cikin 100 na gurbataccen man fetur da kwal da kuma gas na cikin ƙasar ne. Ƙasa ce ta akasarin al'ummar Musulmi amma akwai Rashawa masu yawa amma sune tsiraru.

Me yasa ta ke tashe a labarai? Tarzoma ce ta ɓarke saboda ƙarin farashin man mota, kuma tashin hankalin ya girgiza gwamnatin kasar har ta kai ga wasu jami'an gwamnati na ajiye aiki, kuma ana murƙushe masu zanga-zangar ba sani ba sabo.