Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Desmond Tutu: An soma addu'ar ban kwana da gawar babban malamin coci
Gawar marigayi Archbishop Desmond Tutu ta isa cocin St George's Cathedral da ke Cape Town a Afira Ta Kudu inda za ta kwashe kwana biyu domin mutane su yi ban kwana da ita.
Tutu, wanda ya taba samun lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya kuma ya taimaka wa kasar wajen kawo karshen mulkin wariyar launin fata, ya rasu ranar Lahadi yana da shekara 90.
A hukumance za a yi jana'izarsa ranar 1 ga watan Janairu bayan mutane sun gama ban kwana da gawarsa.
Ana sa ran dandazon jama'a za su ziyarci cocin nasa daga yanzu zuwa kwanaki biyu masu zuwa.
An tsawaita wa'adin ban kwana da shi zuwa kwana biyu "bisa fargabar da ake yi ta samun cunkoso," a cewar wani malamin coci a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP.
Malaman coci sun rika kona turare a yayin da ake shiga da gawar Tutu cikin cocin.
Mai dakin Tutu Leah tabii gawar a hankali a yayin da ake shiga da ita cikin cocin.
Za a bar mutane su shiga ciki domin yin ban kwsana da gawar malamin cocin wanda ake matukar mutuntawa, wanda ya kasance a sawun gaba wajen yaki da gwamnatin wariyar launin fata a Afirka Ta Kudu daga 1948 zuwa 1991.
Za a gudanar da addu'o'i a dukkan fadin Afirka Ta Kudu yayin da abokansa na kurkusa za su yi tasu addu'ar nan gaba.
Idan aka kammala jana'izar Tutu ranar Asabar, za a kona ta sannan a ajiye tokar a cikin cocin, inda ya kwashe shekaru da dama yana wa'azi.