Hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afirka na mako: Daga 17 zuwa 23 ga watan Disambar 2021

An wallafa

Zababbun fitattun hotuna daga nahiyar Afirka da wasu sassan.

Short presentational grey line
Traditional Burundian drummers perform the royal drum dance during the national drummer contest in Gitega, Burundi, on December 20, 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu kidan kalangun gargajiya na kasar Burundi sun fito da karfinsu a Gitega babban birnin kasar ranar Litinin don shiga gasar kasa….
Traditional Burundian drummers perform the royal drum dance during the national drummer contest in Gitega, Burundi, on December 20, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu wasan daka tsalle sama a yayin da masu buga kalangu ke wasa.
Women clad in their traditional Zulu outfits take part during the Indoni SA Cultural Festival on December 18, 2021 in Durban. - The Indoni festival, a three-day feast, showcases traditions of South African provinces and aims to demonstrate unity and the unique diversity of the country.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Har ila yau an gudanar da wasu bukukuwan al'adun gargajiya a Afirka ta Kudu a ranar Asabar yayin da mata sanye da tufafin 'yan kabilar Zulu don wasun nunin al'adun gargajiya a birnin Durban.
Algeria's national football team celebrates on a bus with their fans in Algiers, on December 19, 2021, a day after winning the FIFA Arab Cup 2021. - Africa Cup of Nations holders Algeria won the Arab Cup on December 18, beating Tunisia 2-0 after extra time in Qatar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gudanar da bukukuwa a Algiers babban birnin kasar Algeria ranar Lahadi bayan da kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar ta samu galaba a gasar wasan cin kofin kasashen Larabawa a kasar Qatar, suka dawo gida.
Expired AstraZeneca coronavirus disease (COVID-19) vaccine vials are seen at the Gosa dump site in Abuja, Nigeria on December 22, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Alhamis, wani mai daukar hoto ya dauki hoton wasu kwalaben ruwan allurar rigakafin korona kafin a zubar da zu a cikin bola a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
A Red Cross volunteer holds a Red-cross flag while his colleagues bury the bodies of people killed by Codeco militiamen in the village of Dhedja, December 19, 2021, 60 kilometers from Bunia, the provincial capital of Ituri in northeastern Democratic Republic of Congo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ranar Lahadi wani mai aikin sa-kai na kungiyar agaji ta Red Cross dauke da tutar kungiyar yayin da abokan aikinsa ke binne wasu mutane da aka kashe a wani hari da aka kai a baya bayan nan.
This aerial photograph taken on December 21, 2021 shows the Rhoo IDP camp, 60 kilometers from Bunia, the provincial capital of Ituri in northeastern Democratic Republic of Congo. - Since late November, several villages and IDP camps have been attacked and nearly 100 people have been killed in the area, forcing up to 70,000 people to gather on the Rhoo hill around a base of Bangladeshi peacekeepers from Monusco

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tashin hankali a yankin inda ake kai hari kan sansanoni da kauyuka, ya tilasta wa mutane 70,000 neman mafaka a kusa da wani sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Rhoo, da ake gani a nana a ranar Laraba.
Protesters gather outside the Presidential Palace during a demonstration demanding civilian rule within the 3rd year of the "December Revolution" in Khartoum, Sudan on December 19, 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Game da kasar Sudan, wani mai zanga-zanga Khartoum babban birnin kasar Sudan ya zo da shirin tunkarar hayaki mai saka kwalla a yayin da mutane suka fito don tunawa da zagayiwar shekaru uku tun bayan da aka fara zanga-zangar da ta haddasa kawo karshen mulkin shugaba Omar al-Bashir...
A Sudanese female protestor helps to another one who affected from tear gas as they clash with security forces during protest in front of the main door of the Republican Palace in the capital Khartoum, Sudan, 19 December 2021. Tens of thousands of protesters marched during a demonstration marking the third anniversary of the start of mass demonstrations that led to the ousting of the dictator al-Bashir.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga na taimaka wa wajen rage tasirin hayaki mai saka kwalla da aka harba don tarwatsa dubban daruruwan masu zanga-zanga.
Tunisian security forces intervene in people, who gathered for sit-in protest against Tunisian President Kais Saied's 'extraordinary decisions' in Tunis, Tunisia on December 18, 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yan sanda a Tunis babban birnin kasar Tunisia sun kutsa don dakatar da yunkurin zaman dirshan daga shirya zanga-zanga kan shugaba Kais Saied, wanda ya dakatar da majalisar dokoki na wucin gadi a cikin wata Yuli.
A model has the final touches done to her make up before heading to the catwalk during the 19th Dakar Fashion Week held at the Baobab forest in Nguekhokh, some 70kms south of Dakar, on December 18, 2021

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wata mai yin sana'ar kwalliya na shafa wa wata mai tallar kayan kawa hoda a yayin bikin nuna kayan kawa a kauyen baobab ba kasar Senegal ranar Asabar.
A vendor takes advantage of the Christmas spirit to sell red hats to passing motorists in Harare, Zimbabwe, 20 December 2021.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu talla a bakin hanya a Harare babban birnin kasar Zimbabwe a ranar Litinin na kokarin jan hankalin masu motoci su sayi rigar Santa ko balan-balan din Fada Kirsimeti.
The streets and buildings of the Heliopolis district are decorated with lights and Christmas trees to celebrate the New Year in Egypt, Cairo, December 23, 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Alhamis, a wani bangare na nahiyar, mazauna birinin Alkahira babban birnin kasar Masar sun yi tsayuwar daukar hoton dauki da kan ka a jikin bishiyar Kirsimeti da aka kawata da fitilu.

Duka hotunan na da hakkin mallaka.