Abubakar Malami: Da gaske ministan shari'ar Najeriya ke sarrafa EFCC yadda ya ga dama?

An wallafa

Hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta`annati ta ce tana gudanar da bincike kan zargin cewa ministan shari`ar ƙasar, Abubakar Malami ne yake sarrafa hukumar, sai abin da ya ce ta ke yi.

Binciken EFCC ya shafi wani sautin da ake yadawa ne ta intanet wanda a ciki ake zargin cewa Malami ne yake juya hukumar a binciken da ta ke gudanarwa da ya shafi cin hanci da rashawa.

Hukumar EFCC ta ambato wani jami`inta mai suna Mohammed Idris, wanda ɗan sanda ne kuma ƙwararren lauya cewa shi ne yake tattaunawa da wani da ake zargin cewa mai laifi ne ta waya.

Hukumar ta ce ta saurari sautin da ake magana wanda jaridar Daily Nigeria ta bankaɗo, kuma ta fahimci cewa jami`nta ne yake magana da wani abokin cin mushe ko cuwa-cuwarsa, wanda a ciki yake cewa minstan shara`a Abubakar Malami shi ke da wuka da nama a EFCC, kuma komi girman rikici zai kashe maganar idan aka kama kafarsa, zargin da ministan shara`ar ya musanta.

A martanin da ta mayar hukumar EFCC ta yi tir da dabi`ar jami`in nata, tana cewa ya taka ka`idar aiki, dabi`ar da ta ce sam-sam ba ta dace da farar aniyar hukumar ba a wannan lokacin.

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujeran, a cikin wata sanarwa, ya ce hukumar tana gudanar da bincike a kan wannan zargi, wanda ya ce ba shi da tushe ballantana makama.

Ya ce hukumar ta aiki cikin kariya daga duk wani zai iya yi mata katsalandan daga waje ga ayyukanta.

A cikin sautin, jami'in EFFC da ake zargi Mohammed Idris ya shaida wa abokin maganarsa, wanda hukumar ta rufe masa asusunsa na banki, "cewa a halin da ake ministan shara`a yana sa baki ana buɗe wa miyagu dama da aka rufe masu asusu, komai girman laifin cin hancin da ake zarginsu da aikatawa."

Amma ministan shara`ar Najeriya, Abubakar Malami, ya ce wasu ne kawai suke so su shafa masa kashin kaza.

Mai taimaka masa wajen yaɗa labarai da hulda da jama`a Dr Umar Gwandu ya shaida wa BBC cewa "yarfe ne akwai da labarin ƙanzon kurege ake yaɗawa, kawai an kurɗo da sunan minista ne a cikin zantawar mutanen."

Ministan dai bai faɗi ko da wani irin mataki zai ɗauka nan gaba ba, amma ya ce matakin da EFCC ta ɗauka na gudanar da bincike ya masa dadi.

Sabon hugaban hukumar EFCC, Abdurrashid Bawa ya fito ne daga jihar Kebbi, jihar ɗaya da ministan shari`ar Najeriya, kuma wannan ne ya sa wasu ke tunanin cewa ministan ne ya yi uwa da makarɓiya wajen dora shi a kan kujerar, don haka suke zargin cewa ministan zai iya jujjuya hukumar, amma sabon shugaban ya daɗe da musanta hakan.

An sha ɗora alhakin abubuwa da dama da ke faruwa a Najeriya kan ministan shariar Najeriya, Abubakar Malami.

Ko a lokacin sauya shugaban EFCC Ibrahim Magu an zargi hannun Malamin, haka ma lokacin dirar mikiya da aka yi wa gidan Mai shari'a Mary Odili, da kuma wasu abubuwa da dama da ke faruwa da taƙaddama da ake yawaita samu a gwamnatin tarayya.