Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zamantakewa: Matakan da mace za ta dauka idan mijinta manemin mata ne
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.
A wannan kashi na 24 din, shirin ya yi duba ne kan matakan da mace za ta dauka idan ta samu kanta a jarabawar miji mai neman mata.
Wani babban al'amari da ke lalata aurarraki da zamantakewar ma'aurata a lokuta da dama shi ne cin amanar aure, kamar jarrabar mace da miji mai neman mata, kamar yadda malam ya fada a farkon shirin.
Irin wannan matsala ta zama sanadin mutuwar miliyoyin aurarraki a al'ummarmu, ko kuma ta saka wa wasu hawan jini ko ma ta zama silar yaduwar munanan cututtuka ga wadanda ma ba su ji ba ba su gani ba.
Sai dai abin takaicin duk da wadannan matsaloli sai a ji wasu matan da suka kallafawa ransu matsanancin kishi suna cewa wai da kishiyar gida gara ta waje. Kaico!
Sheikh Dr Abdullah Gadon Kaya, wani malamin addinin Musulunci a birnin Kano da ke Najeriya, ya yi fashin-baƙi a wannan makon kan lamarin.
Ya tabo batun yadda wasu matan kan yi sakaci har mazansu su fara yawon-ta-zubar.
Sannan ya bai wa matan da ke cikin jarabtar shawarwarin da muke fata su zama mafita, tare da gargadi ga maza masu irin wannan halin.