Kin amincewar Buhari da zaben 'yar tinke ya tayar da kura a Najeriya

An wallafa

Matakin shugaba Buhari na ƙin sanya hannu kan kuɗirin dokar zaɓe da majalisar dokoki ta amince na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya.

Batun zaɓen ƴar tinke ne ya fi jan hankali a kuɗirin dokar, kuma Shugaban ya bayyana dalilansa na ƙin sanya hannu, a wasiƙar da ya rubutawa majalisa, inda ya ce zaben 'yar tinke zai lakume kuɗi da kuma bayyana fargabar ƙalubalen tsaro wurin gudanar da shi.

Sai dai wannan matakin ya haifar da mahawara a shafukan sada zumunta inda wasu ke goyon bayan shugaban, wasu ƴan ƙasar da ƙungiyoyin fararen hula kuma ke sukar matakin tare da yin kira ga majalisa ta yi gaban kanta ta amince da kuɗirin ko da shugaban ya ƙi sa hannu.

Tuni Majalisar dokokin kasar ta amince da dokar da ta ƙunshi amincewa da batun zaɓen fid da gwani ta hanyar ƴar tinƙe wanda aka fi sani da ƙato bayan ƙato. Kuma dama shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kawai ake jira ya sanya hannu a kuɗirin domin ya zama doka, kuma yanzu ya ƙi sanya hannu.

A zaman da suka yi ranar Laraba majalisun dokokin kasar sun tabbatar da cewa shugaba Buhari bai sanya hannu a kan kudurin dokar zabe da suka mika masa ba tare da karanta dalilansa a zauren majalisun.

Buhari da majalisar tarayyar Najeriya na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafukan sada zumunta musamman a Twitter a ranar Talata.

Ƙungiyoyin fararen hula da kare haƙƙin ɗan Adam kamar CISLAC a cikin wata sanarwa ta buƙaci majalisar tarayya ta hau kujerar naki ta ƙi amincewa da matakin shugaban game da batun dokar zaɓen.

Amma batun ya janyo mahawara kan ikon da majalisa take da shi na yin watsi da matakin shugaban.

Abin da ƴan Najeriya ke cewa:

Ƴan Najeriya da dama na bayyana ra'ayoyi ne mabanbamta, inda wasu ke bayyana goyon bayan dalilan shugaba Buhari wasu kuma na ganin matakin kin amincewa da sabon tsarin zaɓen kamar tsohe wa mutane shiga zaɓuka ne a duka matakai.

Wasu kuma sun mayar da hankali ne kan matakin da majalisa za ta ɗauka bayan shugaba Buhari ya ƙi sanya hannu, kamar tambayar da @Jemce ya yi wa majalisar dokokin ƙasar.

@Allibaloo a cewarsa: "Zaɓen ƴar tinke ya shafi wanda ke iya tara ƴan daba. Babu wani adalci a cikin tsarin."

Sai dai @TupacXShakur ya mayar masa da martani inda ya ce "zaɓen wakilai shi ne wanda zai iya tasirin sakamako ta hanyar kuɗi da ƙarfin iko. Ina goyon bayan ƴar tinke"

A ra'ayin @OluAdenodi: "Majalisa kawai ta yi watsi da sa hannunsa. Amma na san ƴan majalisa ba za su yi domin ƴan amshin shatan shugaba Buhari ne. Abin kunya ne muna da gwamnati da ƴan majalisar da ba su da hangen nesa"

@nafeezi a ra'ayinsa cewa ya yi "batun bayyana sakamako ne ta intanet abin fargaba ba zaɓen ƴar tinke ba. Majalisa ra'ayinsu ɗaya na yin watsi da kuɗirin zaɓen ta hanyar amfani da ƴar tinke a matsayin dalili.

Amma mu jira mu ga yadda majalisa za ta kasa hawa kujerar naƙi."