Isra'ila ta yi shuri da zargin shugabannin kiristoci a Ƙudus

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Isra'ila ta yi shuri da zarge-zargen wasu shugabannin Kiristoci a birnin Ƙudus, na cewa wasu ɓata gari na neman tashin su daga birnin.

Shehunnan malaman coci-cocin a Kudus sun ce mahukunta sun zura ido suna kallo ana cin zarafin Kiristoci da lalata wurarensu.

Archbishop na Canterbury ya ce ba a yi tsammanin sanarwar ba, don haka akwai bukatar duba lamarin.

Sai dai mahukuntan Isra'ila sun bayyana ta a matsayin mara tushe.

Yayin da adadin larabawan Falasɗinawa Kiristoci ke ƙaruwa a gaɓar yammacin kogin Jordan, ana ci gaba da nuna musu wariya tsawon shekara da shekaru.

A yanzu dadadin Kiriscocin da suka rage a Gaɓar Yamma Kogin Jordan bai wuce kashi biyu cikin 100 ba, wato jimillar mutum dubu biyu kenan suka rage a birnin na Ƙudus.

Cikin wata sanarwa da shugabannin cocin da ke birnin Ƙudus suka fitar, sun yi gargadin cewa tun 2012 ake samun cin zarafin Kiristoci har ma da jagororinsu, da kuma kai hari kan wuraren ibadarsu.

''Irin waɗannan ɓata gari na kai waɗannan hare-hare da zummar razana Kiristoci don su fice su bar birnin da sauran wurare masu tsarki'' inji sanarwar.

Sun amince da kokarin mahukuntan Isra'ila na ba wa kiristoci kariya a tasirin da ake da shi na tilasta musu barin birnin.

Cikin wata mukala da ya rubuta a jaridar Sunday Times, Archbishop na Canterbury wanda ke jagorantar kiristoci kusan miliyan 80 mabiya ɗarikar Anglika a duniya, ya goyi bayan sanarwar da shugabannin cocin suka fitar wadda ke gargadi kan cewa wani mummunan al'amari a tarihi na maimata kansa.

Ya yaba wa damar samun yancin yin addinin da Kiristoci ke yi a Isra'ila, sai dai irin abubuwan da suke faruwa a kwana-kwanan nan na uzzurawa musu a wasu yankuna abun tayar da hankali ne.

Ya kara da cewa rashin samun damar watayawa a gabar yammacin kogin Jordan da Kiristoci ke yi sanya an keɓe su daga cikin al'umma, wani abu da ke janyo taɓarɓarewar tattalin arzikinsu.

''Babu buƙatar faruwar irin waɗannan al'amura, za a iya shawo kansu, sai dai akwai bukatar ɗaukar mataki cikin gaggawa, muna ba wa mahukunta ƙwarin guiwar su ɗauki matakin da ya dace'' kamar yadda ya ambata cikin waccan muƙala.

Cikin wata sanarwa da gwamnatin Isra'ila ta fitar ranar Litinin, ba ta yi martani ga mukalar da Archbishop na Centerbury ya rubuta ba, amma ta ce bayanin da shugabannin cocin ta Kudus suka yi ƙarya ce kawai tsagwaronta, kuma sabanin abun da ke faruwa a zahiri.

''Shugabannin addinai na da muhimmiyar rawar takawa a harkar ilimi da kuma amincewa da ra'ayin juna da samar da hadin kai a tsakanin jama'a, don haka abun da ya kamata su fahimta kenan su kuma tsaya a matsayinsu, su kuma kaucewa irin waɗannan kalamai da ka iya haifar da rikici a tsakanin jama'a'' inji sanarwar.

Sanarwar ta kuma zargi malaman da yin shiri a kan irin cin zarafin Kiristoci a fadin kasashen Gabas ta Tsakiya.

Har yanzu dai babu wani tartibin martani daga limaman cocin gargajiyar ta Ƙudus, amma wani mai magana da yawun Archbishop na Canterbury ya ce ya sha yin magana a kan irin cin zalin da ake yi wa kiristoci a yankin