Yaro rike da taya da dodanni suna cikin hotunan Afirka na wannan mako 10-16 Disamba 2021

An wallafa

Wasu daga cikin kyawawan zababbun hotunan Afirka da na wasu ƴan nahiyar a sauran sassan duniya a wannan makon.

Short presentational grey line
Mace sanye da tufafin garhajiya mai launuka daban-daban, ta rufe fuskarta dahannunta, ya yin da launin sararin samaniya da ke bayan ta ya kara kawata hoton.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tallan kayan kawa da aka yi a birnin Nairobi na kasar Kenya, a ranbar Asabar, wata mace ta rufe fuskarta saboda kaucewa kamarar daukar hoto
Mutum sanye da tufafin gargajiya, dauke da kahon da ya ke amfani da shi wajen kida a hannunsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A dai wurin bikin wani mawakin gargajiya ya baje kolin abin kidansa.
Mutum sanye da kayan dodanni, kayan na reto a jikinsa ya yin da yara ke zaune su na kallo.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A jihar Ogun da ke Najeriya, mutum cikin shigar dodanni na tsaye gaban yara a ranar Laraba.
Sarauniyar kyau ta Namibia sanye da doguwar riga mauo launin Ja ta na tafiya cikin kwalisa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Isra'ila, sarauniyar kyau 'yar Namibia na tafiya a layin dogon da ke cikin dakin taro, a wajen zaɓen sarauniyar kyau a ranar Juma'a ...
Wakiliyar Ghana a taron sarauniyar kyau, sanye da korran tufafi, da hular da aka yi da gashin wani tsunts. Ta yi tsayuwa mai ban sha'a ta hanyar daga hannu daya, da nade daya a cikin ta, idanun ta na kallon sama cikin salo mai daukar hankai.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ga kuma Miss Ghana ta yi tsayiwa mai ban sha'awa a wajen taron..
Saruniyoyin kyau uku tsaye a kan dandamali. Kowacce sanye da kyakkyawan tufafin mai tsananin kyau da kyalkyali, domin daukar hoto

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Saruniyar kyau ta Afirka ta Kudu, Lalela Mswane ita ce ta zo ta uku, duk da cewa gwamnatin kasarta ta umarci ta kauracewa taron saboda nuna kin goyon bayan abin da Isra'ila ke yi wa Falasdinu.
Wani mutum da babu riga a jikinsa, rike da kakkaifar wuka ya na datsa kashi da na nama a kusa da matakalar bene.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Can a kasar Brazil, a ranar Litinin, wani dan Congo ne ke faskara ƙashi.
Mace na motsa shinkafa. Ga kuma manyan robobi a bayanta.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba a kasar Senegal, wata mata ke dafa shinkafa dahuwar gidan buki mai suna thieboudienne, wato shinkafa da kifi, a wata katuwar tukunya. Nau'in abincin ya shiga jerin kayan tarihi na hukumar UNESCO.
Dan Tunusia mai saida lemon tsami

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A kasar Tunisiya wani dan kasuwa ne ya baje kolin hajarsa ta lemon tsami a wata kasuwa.
Wani yaro abakin ruwa ya yi alkantara a sama. Ya yin da sararin samaniya ta ke dauke da launin ruwan toka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai wannan rana amma a birnin Benghazi na kasar Libya, wani yaro ya yi alkantara a kokarin koyin wani salon wasa mai suna Parkours.
Maza biyu na wasan ninkaya, sanye da tabarau na ido d ake amfani da shi a ninkaya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ci gaba da wasanni a Abu Dhabi a ranar Alhamis, dan wasan Masar E Youssef Elkamash na fafatawa a zagaye na karshe na gasar wasan ninkaya ta duniya.
Yaro ya yi wa fuskarsa fenti da launin fari, daure da jan adiko, ya leko da fuskarsa tsakanin tayar da ya yi mata fenti da launuka daban-daban.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Idan muka koma Najeriya, a ranar Lahadi wani yaro na gudanar da wasa a wajen wani taro a birnin Lagos...
Mata sanye da tufafin gargajiyam, da murzani da tsakiya a hanny da wuya da kawunansu, zaune akan dogon benci. A hannayensu su na rike da gorar duma da aka kawata da duwatsu masu launi daban-daban.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, TMata na gudanar da bikin murnar dawo da kayan tarihi da aka sace a birnin Benin......

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.