Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Likitocin ƙwaƙwalwa da masu ilimin roka ba su fi sauran mutane basira ba - Bincike
Kuna tunanin zama likitocin ƙwaƙwalwa ko masu haɗa kumbon zuwa sararin samaniya? E kuna da dama.
Sai dai masu irin waɗannan sana'o'in ba lallai ne sun fi sauran mutane basira ba, a cewar wani bincike.
Masu bincike sun nemi injiniyoyin sararin samaniya 329 da likitocin ƙwaƙalwa 72 su gudanar da wasu ayyuka da zimmar gwada basirarsu.
Sakamakon da aka wallafa a mujallar British Medical Journal bai nuna wani bambanci mai yawa ba tsakaninsu da sauran al'ummar Birtaniya.
Masu binciken sun ce aniyarsu ita ce su gane masu wace sana'a ce suka fi hazaƙar ƙwaƙwalwa.
Sannan suna son su gano ko fahimtar sauran mutane game da masu sana'o'in biyu ta dace da gaskiya.
Yayin da ake hasashen sashen biyu za su rasa ma'aikata cikin shekara 10 mai zuwa, masanan suna ganin jarraba wasu hanyoyin za su taimaka wajen ɗaukar mutane aiki a ɓangarorin kimiyya.
An auna fahimtar mutanen ɓangarorin biyu ta intanet a sashe shida na fahimta, ta hanyar amfani da wani tsari na 'Great British Intelligence Test' da aka ƙirƙira a Kwalejin Imperial ta Landan.
Jarrabawar ta ƙunshi ɓangaren ma'adanar bayanai ta ƙwaƙwalwa da mayar da hankali da kula da yanayi. Kazalika, an tambayi mutanen game da shekarun haihuwarsu da jinsi da kuma ƙwarewarsu a wurin aiki.
Sai aka kwatanta sakamakon ɓangarorin biyu da wasu bayanai da aka tattara daga sauran al'ummar Birtaniya 18,000.
An gano cewa likitocin ƙwaƙwalwa sun fi injiniyoyin roka ƙoƙari wajen fayyace ma'anar abubuwa, kamar samar da ma'anar kalmomin da ba a saba ji ba.
A gefe guda kuma, injiniyoyin sun fi takwarorinsu likitoci ƙoƙari wajen tsayar da hankali da kuma wasa da hankalin mutum kamar jujjuya hotuna a ƙwaƙwalwar mutum.
Idan aka kwatanta da sauran jama'a, injiniyoyin ba su nuna wani bambanci ba a kowane ɓangare.
Likitocin ƙwaƙwalwa kuma sun taɓuka a sashe biyu kacal: sun fi sauri wajen warware matsala, amma kuma ba sa iya tuna abubuwa da wuri.
Masu binciken sun ce ƙila hakan na da nasaba da "yadda ake gudanar da tiyatar ƙwaƙwalwa cikin sauri, ko kuma ta iya yiwuwa saboda an saba ba su horo kan warware matsala cikin sauri a lokuta masu hatsari".
"Babu mamaki cewa an ɗauki injiniyoyin da likitocin a matsayin ababen koyi fiye da kima," in ji binciken.
Ya ƙara da cewa: "Ya kamata sauaran sana'o'i ma a ɗora su kan irin wannan mizanin sannan ya kamata bincike na gaba ya duba sana'ar da ta fi wata."