Mummunar guguwa ta hallaka sama da mutum 100 a Amurka

An wallafa

Shugaba Biden na Amurka ya ce guguwa mai ruwa da ake fama da ita a kasar a yanzu, wadda ta fada wa jihohi shida tare da hallaka gomman mutane ita ce mafi girma a tarihin kasar.

Akalla sama da mutum 100 ne zuwa yanzu ta hallaka a jihar Kentucky kadai, inda ta share garuruwa da kauyuka kacokan.

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta yi duk abin da za ta iya domin taimaka wa yankunan da guguwar ta yi barna.

Ba karamar barna wannan guguwa da ke mamayar jihohin na Amurka ta yi ba, inda ta share garuruwa gaba daya, ta mayar da gidaje da gine-gine tarin buraguzai.

Hukumar kula da yanayi ta kasar ta ce ta samu rahotannin gagarumar guguwar har 36, inda ta farma jihohin Illinois da Kentucky da Tennessee da Missouri da Arkansas da kuma Mississippi.

A birnin Mayfield da ke jihar Kentucky guguwar ta fada wa wata ma'aikatar yin kyandir da daddare a lokacin da mutane kusan 110 ke cikin aiki, inda mutum 40kadai aka samu da rai, ta kuma lalata ginin gaba daya.

Ana dai ci gaba da gagarumin aikin nema da kuma ceto, ko da za a dace da wasu da ke da sauran numfashi.

Gwamnan jihar Andy Beshear (Bee-sheer) ya ce lamarin ya munana babu kyawon gani, za su rasa rayuka da yawa, a ce gini mai girma kamar wannan ya zube gaba daya.

Yanayin da ake ciki dai babban kalubale ne ga hukumomi, domin ya kai ga dubban mutane ba su da wutar lantarki da ruwa.

Shi kansa ofishin 'yan sanda na garin Mayfield guguwar ta bannata shi kuma 'yan kwana-kwana sun rasa kayan aikinsu, abin da ya kawo cikas ga kokarinsu na kai dauki.

A Illinois, akalla mutum biyu ne suka mutu a lokacin da guguwar ta wargaza gidan adana kayayyaki na kamfanin Amazon.

Can kuwa a Arkansas guguwar ta fada wa wani gidan kula da tsofaffi ne, inda ta kashe mutum daya ta kuma raunata da yawa.

Shugaba Biden ya ayyana dokar ta-baci a Kentucky, tare da alkawarin bayar da duk taimakon da ake bukata domin mutane su farfado daga abin da ya kira, mummunan bala'in da ya wuce tsammani:

"Hukumar bayar da agajin gaggawa na nan tana aiki tare da kowace jiha domin tantance barnar da ta auku da kuma mayar da hankali kan tallafin tarayya, inda aka fi bukatarsa da kuma yadda za mu samu zuwa can da sauri.'' Inji Biden.