Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ra'ayin shugabannin addinai ya bambanta kan cire wa Najeriya takunkumi
Shugabannin addinai na ci gaba da bayyana ra'ayoyi masu sabani da juna tun bayan matakin da Amurka ta ɗauka na cire Najeriya daga cikin jeren ƙasashen da ta yi wa baƙin fenti kan tauye 'yancin addinai.
A ranar Laraba ne Amurka fitar da jerin sunaye na wannan shekara na kasashen da take zargi da tauye 'yancin addini, gabanin ziyarar da Sakataren Harkokin Wajenta Anthony Blinken ya kai Najeriya.
Sai dai da alama wannan mataki na Amurka bai yi wa wasu shugabannin addinai a Najeriya daɗi ba, kamar yadda wasu Kiristoci a Najeriyar ke nunawa.
Kiristocin sun ce Amurka ba ta samu sahihan bayanai kafin yanke wannan shawara ba, don kuwa a cewarsu har yanzu akwai matsalolin tauye 'yancin addini a ƙasar.
Sai dai wasu Musulmai sun shaida wa BBC cewa matakin abin a yaba ne, kuma ya dace don a cewarsu a hukumance ba a cika samun tursasa wa mutum saboda aƙidarsa ta addini ba.
Muhawarar da ɓangarorin biyu ke tafkawa
Rabaran Murtala Mati Dangora wanda mataimakin shugaban kungiyar Kiristoci reshan jihar Kano ta CAN a Najeriya ne, ya ce har yanzu akwai takurawa da tauye 'yancin addinai a wasu sassan ƙasar, musamman kan batun gina wuraren ibada.
Ya ce idan dai Amurka ta cire wannan takunkumi, babu mamaki sun samu karkataccen bayani ne, domin har yanzu ana tauye 'yancin addini da hana wasu abubuwa.
Sai dai a nasa ɓangaren wani limamin addinin Musulunci kuma ɗan kwamitin tattaunawa tsakanin addinai, Muhammad Nurul Khaleed, ya ce la'akari da matakin tarayyar kasar ba a fiye samun takurawa ko tsangwama kan wasu rukunin mutane ba game da addininsu.
Amma ya ce idan aka lura a gwamnatance babu batun tursasawa duk da cewa ba a rasa korafi, amma hakan sai dai a jihohi aka fi samun matsala.
Shi kuma Rabaran Murtala cewa yake, wajibi ne gwamnati ta bai wa kowa dama 'yancin addininsa yadda ya kamata, idan Kirista na son gina coci ko daukar aiki kowanne abu a ba shi dama ba tare da la'akari da addini ba.
Malam Nurul Khaleed, a nasa tsokacin ya ce zaman lafiya ba ya tabbatuwa sai an mutunta addinai, shugabanni da malamai su haɗa karfi da karfe wajen tattauna duk wata matsala.
Yana mai jadada cewa hakan shi zai samar da mafita da daidaito wajen cigaban al'umma.
Abin da gwamnati ta ce
Gwamnatin Najeriya dai ta ce batun sanya sunan kasar tun da fari a wannan jeri na kundin baƙin fentin Amurka sharrin masu rajin a-ware ne kan yaƙi da Boko Haram.
Sannan ta ce matsalolin rikicin Boko Harama aka yi amfani da su wajen sanya sunan Najeriya a kundin, bayan danganta cewa hare-haren mayakan na karewa kadai ne kan Kiristoci.
Gwamnati a ta bakin kakakin fadarta, Malam Garba Shehu ta ce sanin kowa ne cewa hare-haren mayakan Boko Haram bai raga wa Musulmi ko Kirista ba.
Haka kum gwamnati ba ta taɓa zuba ido tana kallo ba tare da daukan mataki ba, a cewar Malam Garba Shehu.
Sai dai duk da hakan malaman manyan addinan Najeriya biyu sun yi tarayya a kan cewa kasar tana da sauran tafiya wajen tabbatar da cikakken 'yancin addini musamman a matakin jihohi.
Malaman biyu dai na ganin inganta 'yancin addini ba tare da tsangwama ko takurawa ba zai bunkasa da kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasa fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban da cigaba mai dorewa.