Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko ana yin ingantaccen gwajin korona ga jami'an Sudan Ta Kudu?
- Marubuci, Daga Nicola Morrison
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Monitoring
- An wallafa
Wani bincike da gwamnatin Sudan Ta Kudu ta gano cewa akwai yiwuwar ba a yi wa jami'anta gwajin korona da kyau ba kafin su yi tafiya zuwa Qatar.
An tilasta wa Shugaba Silva Kiir soke tafiyarsa zuwa Qatar a watan Nuwamba bayan jami'ansa da dama waɗanda suka riga shi tafiya aka tabbatar da suna ɗauke da cutar korona a lokacin da suka isa.
Wani bincike da gwamnatin Sudan Ta Kudun ta yi ya gano cewa da dama daga cikin manyan jami'an suna ba ma'aikatan ɗakin gwajin umarnin su yi musu gwajin baki kawai ban da hanci wanda hakan ba lallai ya bayar da sakamako ingantacce ba.
A martanin da aka mayar kan abin da ya faru a Doha, mataimakin shugaban ƙasar, Hussein Abdelbag ya yi wani jawabi a talabijin na ƙasar wanda ya yi magana kan kawo ƙarshen halayyar da ake da ita ta tafiya ba tare da shaidar tabbatar da cewa mutum ya yi riga-kafi ba tare da shan alwashin zai hukunta duk wani jami'in lafiya da ya bayar da shaidar ƙarya.
Bayan jawabin da mataimakin shugaban ƙasar ya yi, kafafen watsa labarai na ƙasar suka soma bayar da rahoton cewa jami'an sun bar Juba babban birnin ƙasar ɗauke da shaidar yin gwaji ta jabu da ke nuna cewa ba su da korona.
Babu wani tabbaci da ke nuna cewa waɗannan jami'an ba a yi musu gwaji ba, ko kuma ba a yi musu gwajin da kyau ba.
Sabon matakin daƙile shaidar riga-kafin bogi
Mai magana da yawun ma'aikatar lafiya na ƙasar, Mabior Kiir Kudior, ya shaida wa BBC cewa jami'an da suka je Qatar ɗin ba su je da shaidar bogi ba.
Sai dai rahoton da ake yi na bayar da shaidar gwajin korona ta bogi lamari ne da aka daɗe ana yi a Sudan Ta Kudu, wanda saboda tsananin yadda ake tattaunawa a kan batun ya sa aka dakatar da bayar da shaidar gwajin korona ta wucin gadi a Yunin bara, inda aka ɓullo da sabuwar hanyar bayar da shaidar ta amfani da na'ura.
An fito da sabon tsarin amfani da QR code da barcode domin ya kasance abu mai wahala a yi na bogi.
Med Blue, wanda wani wurin yin gwaji ne a filin jirgin Juba na ɗaya daga cikin wurare a Sudan Ta Kudu da aka yarje mawa su yi gwajin cutar korona.
Kamar yadda Eye Radio ta bayyana, a farkon shekarar nan an tare wasu matafiya a iyakar ƙasar da Uganda ɗauke da shaidar bogi ta gwajin korona wadda a jikinta aka saka tambarin Med Blue.
Sai dai wajen yin gwaji na Med Blue ya musanta wannan zargin tare da bayyana cewa akwai yiwuwar na bogi ne.
Dakta Poles Simon daga Med Blue ya shaida wa BBC cewa sabon tsarin da aka fitar ya haɗa da cewa: Dole ne waɗanda za su je wajen gwaji na Med Blue su je da katin shaidar su na ɗan ƙasa kuma sai an tantance mutum kafin a ba shi sakamakon gwajinsa.
Kamar yadda Mista Simon ya bayyana, ɗakunan gwaji na Med Blue na yawan samun ziyara daga jami'an gwamnati domin tabbatar da cewa komai na tafiya daidai. Yana ganin cewa tsarin da aka fito da shi na amfani da barcode zai kawar da duk wata hanya ta yin sakamakon na bogi.
Ya kuma ƙara da cewa a halin yanzu akwai wurare takwas da ke gudanar da gwajin korona a ƙasar da kuma dagewa kan cewa ba a wurin gwajinsu bane aka yi wa jami'an gwamnatin Sudan gwajin korona.
Sudan Ta Kudu dai na daga cikin ƙasashen duniya waɗanda ba su da ci gaba, kamar yadda wani bincike ya nuna, inda aiwatar da riga-kafin korona a ƙasar yake fuskantar ƙalubale ciki har da tsada da kuma rashin samun allurar.
Ƙasar ce take da adadi mafi ƙaranci na waɗanda aka yi wa riga-kafi a duniya inda ƙididdiga ta nuna cewa kashi 1.2 cikin 100 na ƴan ƙasar kacal aka yi wa riga-kafin korona.