Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Abubakar Kacallah
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Sheikh Muhammad Abubakar Kacallah daga jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.
An haifi malamin a ƙauyen Sandari a kusa da garin Bama da ke bakin kogi a shekarar 1956.
Amma ya girma a garin Taswari har ya kai shekara hudu, daga nan sai aka mayar da shi wajen kawunsa. "Da na kai shekara 10 sai na koma wajen dangin mamata inda na ci gaba da karatu," in ji shi.
A 1973 ne ya koma birnin Maidiguri wajen Malam Aminu Gwani Hassan Altoto inda ya yi sauka ta biyu a wajensa, ya kuma fara karatun fannonin ilimi a wajen malamai daban-daban kamar su Goni Mamman Kwaterema da Goni Bukar Goterama da Goni Shettima da sauran su.
Surorin da suka bai wa malam wahala a lokacin da yake karatu su ne Suratu Rahman da Suratu Anbiya "amma a lokacin yarinta ce ta sa suka ban wahala."
Surorin da ya fi jin dadin karanta su kuma su ne Suratu Sab'i da Suratu Sajda.
'Abin da ba zan manta ba'
"A rayuwata akwai lokacin da na yi aure a 1982, na shiga karatun Higher Islamic, shi kenan sai aka sallame mu. Ga iyali ga gidan haya ga rashin aiki.
"Akwai wani bawan Allah da aka ba shi labarin halin da nake ciki, Alhaji Tijjani Bolori sai ya aika na je. Ya kira kaninsa ya ce a duk lokacin da kaya ya fita daga kamfaninsa to a cire a ba ni.
"Tun daga lokacin nan kuwa idan kayan masarufin suka fito sai a ba ni, ni kuma sai ƴan kasuwa su karba su ban kudin.
"Gaskiya wannan taimakon ba zan taba mantawa da shi ba," kamar yadda malam ya ce.
Tashin hankali
Sheikh ya ce babban tashin hankalinsa bai wuce na rasuwar mahaifinsa ba, wanda ruwa ne ya tafi da shi ya rasu.
"A lokacin da ina yaro, duk sanda na ji yara suna cewa Baba sai na cewa babata 'ni ina nawa baban?' sai ta ce 'ya rasu,' sai na fashe da kuka.
Ci gaba da karatu
Bayan da malam ya kammmala Higher Islamic sai ya shiga wata makarantar ya yi diploma a 1993.
Sannan ya je Jami'ar Maidiguri ya yi digiri. Ya samu gurbin ƙaro karatu a Sudan a Madani a Jami'ar Jazira inda ya kammala digiri na biyu a can.
Bayan nan ne sai gwamnan Borno na wancan lokacin ya ba shi matsayin babban limami a Jami'ar jihar Borno.
Ana haka kuma ya samu gurbin karo karatu na digirin-digirgir a Sudan.
Malam yana da 'ya'ya 24 rayayyu, idan an hada da wadanda suka rasu sun haura 30. Ina da mata huɗu da kuma jikoki da dama.
Abincin da ya fi so shi ne burabusko da miyar yakuwa.
Malam ya ce har yanzu idan ya tuno da kuruciyarsa yakan samu nishadi sosai.












