Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matafiya 'yan Najeriya sun nuna bacin rai kan matakin da Saudiyya ta dauka
A bayane ta ke cewa matakin da Saudiyya ta dauka na dauka na hana 'yan Najeriya zuwa kasar ya ba 'yan Najeriya da dama mamaki musaman wadanda suka kamala shirye shiryen yin tafiya zuwa kasar.
Akwai daruruwan 'yan Najeriya da ke shirin zuwa kasar domin yin Ummarah , wasu kuwa dan harkokin kasuwanci.
Matakin ya sa matafiya da dama djirsinsu zai tashi ranar Alhamis sun makale a filin jirgin saman Malam Aminu Kano yayin da labarin soke jirginsu ya bayanna.
Fasinjojin, wadanda suka taru a filin jirgin saman sun nuna rashin gamsuwa da wannan mataki.
Sai dai wannan mataki da mahukuntan Saudiyya suka dauka ya jefa dama daga cikinsu cikin damuwa.
Daya daga cikin su ya shaidawa BBC cewa a ranar Alhamis ne jirginsa ya kamata ya tashi domin zuwa Saudiyya amma kwatsam sai suka ji wannan labari kuma cewarsa matakin ya dagula masa lisafi
"Ka riga ka tsara komai, ka je ka yi canji ka shirya komai amma lalata ma tsari, ni wannan alamari na ibada ya su ke son su yi da mu ne" in ji shi.
Matafiyan sun kuma ce matakin ya shafi umrah da suka yi niyya yi kuma sun tafka asara.
A cewarsa: "Allah kadai ya san asarar da na tafka sanadin wannan mataki"
Sai dai matafiyan sun nuna damuwa akan matakin zai iya shafar aikin hajji badi
Saudiyya ta dauki wannan matakin saboda ɓullar sabon nau'in cutar korona na Omicron.
Wannan mataki da Saudiyya ta ɗauka ya sa ta zama ƙasa ta uku a baya-bayan nan da ta hana jirage daga Najeriya shiga ƙasashensu, baya ga Canada da Birtaniya.
Gwamnatin kasar ta ce:: "Mun dakatar da shigar jirage ƙasarmu daga Najeriya, kuma mun dakatar da shigar duk wani ɗan Najeriya Suadiyya walau kai tsaye ko kuma ta hanyar yada gajeren zango a wata ƙasar.
"Sai dai za a ɗaga ƙafa ne kawai ga waɗanda suka yada zango na tsawon kwana 14 a wata ƙasar bayan fitarsu daga Najeriya, sannan ne za a iya barin su shiga Saudiyya," in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta ce ga ƴan Saudiyyan kuma daga suka shiga ƙasar daga Najeriya, to sai sun yi zaman killacewa na kwana biyar ko da kuwa suna da shaidar kammala riga-kafi.
Tun bayan da Saudiyya ta ɗage takunkumin shigar aikin Umara ƙasarta ne ƴan Najeriya suke ta rububin zuwa musamman a watan Oktoba da Nuwamba.
A ranar 16 ga watan Oktoban 2021 ne hukumomin da ke kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain, suka sanar da soke dokar bayar da tazara da aka tilasta a Masallacin Ka'aba a Makkah da kuma na Annabi a Madina.