Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An cafke mutumin da ke da hannu a kisan Jamal Khashoggi
'Yan sanda sun ce an kama wani dan kasar Saudiyya da ake zargi da hannu a kisan dan jarida Jamal Khashoggi a Faransa.
An kama Khaled Aedh Alotaibi a filin jirgin sama na Charles de Gaulle da ke birnin Paris ranar Talata, kamar yadda wata majiyar 'yan sanda ta shaida wa BBC.
Ana kyautata zaton yana daya daga cikin 'yan Saudiyya 26 da Turkiyya ke nema ruwa a jallo kan kisan.
Daga bisani wani jami'in Saudiyya ya ce an yi kamen ne bisa kuskure, kuma an hukunta wadanda ke da hannu a kisan a Saudiyya.
Gidan rediyon RTL ya ce Mista Alotaibi, mai shekaru 33, wanda tsohon mai gadin masarautar Saudiyya ne, yana tafiya ne da sunansa kuma an tsare shi.
An kashe Khashoggi, fitaccen mai sukar gwamnati a Saudiyya, a karamin ofishin jakadancin kasar da ke Istanbul a watan Oktoban 2018.
Saudiyya ta ce an kashe tsohon ma'aikacin jaridar Washington Post a wani hari da wata tawagar jami'an tsaro da aka tura domin lallashinsa ya koma kasar.
Sai dai jami'an Turkiyya sun ce jami'an sun yi aiki ne bisa umarnin manyan jami'an gwamnatin Saudiyya.
Kisan ya janyo ce-ce-ku-ce a duniya kuma ya shafi martabar yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman. Sai dai ya musanta zargin cewa ya na da hannu a kisan.
Wata kotu a kasar Saudiyya ta yanke wa wasu mutane takwas da ba a bayyana sunayensu ba da laifin kisan kai a shekarar 2019. An samu biyar daga cikinsu da laifin shiga cikin kisan kai tsaye tare da yanke musu hukuncin kisa wanda daga baya aka yi mu su sassauci zuwa daurin zaman gidan yari na shekaru 20, yayin da wasu uku aka daure shekaru 7 zuwa 10 a gidan yari domin sun yi wa al'amarin rufa -rufa.
Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman Agnès Callamard ta yi watsi da shari'ar Saudiyya a matsayin "abin da ya saba wa adalci".
A cikin wani rahoto da aka fitar a shekarar 2019, Ms Callamard ta kammala da cewa Khashoggi ya kasance "wanda aka yi wa kisan gilla da gangan" wanda gwamnatin Saudiyya ke da alhakinsa.
Kamen na ranar Talata na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zama babban shugaban kasashen yammacin duniya na farko da ya gana da yarima mai jiran gado na Saudiyya tun bayan kisan Khashoggi.
"Mun yi magana a kan komai, ba tare da wani shinge ba kuma a fili mun tattauna kan batun kare hakkin bil'adama," Mista Macron ya fadawa manema labarai a ranar Asabar.
Abin da mu ka san ikan mutumin da ake tuhuma
Rahoton Ms Callamard ya ce masu gabatar da kara na Saudiyya sun ba da umarnin kama Mista Alotaibi a wani bangare na binciken da ake yi kan kisan Khashoggi, amma daga karshe sun yanke shawarar ba za su tuhume shi ba.
Rahoton ya bayyana Mista Alotaibi a matsayin mamba na rundunar tsaron masarautar, wani bangare na sojojin Saudiyya.
Rahoton ya ce an gan shi a gaban Yarima mai jiran gado a ziyarar da ya kai Amurka a shekarar 2017.
Rahoton ya ce Mista Alotaibi ya isa Istanbul ne a ranar 2 ga Oktoba kuma yana gidan waji jami'in ofishin jakadancin Saudiyya a lokacin kisan Khashoggi, ba cikin karamin ofishin jakadancin ba.
Saudiyya ta ki amincewa da bukatar mika Mista Alotaibi zuwa Turkiyya, inda ake tuhumarsa ba ya nan a birnin Istanbul bisa zargin kisan kai.
Sai dai a ranar Talata, wata majiyar 'yan sanda ta tabbatar da cewa hukumomin Faransa sun aiwatar da sammacin kame na Turkiyya. An kama Mista Alotaibi ne a lokacin da yake shirin shiga jirgi zuwa Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya.
Ms Callamard, wacce a yanzu ita ce sakatariyar kungiyar Amnesty International, ta fada a wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter cewa kamen "ka iya zama wata babbar nasara a kokarin tabbatar da adalci".
Hatice Cengiz, budurwar Khashoggi a lokacin da aka kashe shi, ta yi maraba da kamen kuma ta bukaci Faransa da ta " da ta gurfana da shi gaban kuliya , ko kuma ta mika shi ga wata kasa da ke da ikon yin hakan"
Yadda aka kashe Jamal Khashoggi
Dan jaridan mai shekaru 59, wanda ya yi gudun hijira na kansa a Amurka a shekarar 2017, ba a sake ganinsa ba tun bayan lokacinda ya shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya a ranar 2 ga Oktoba 2018.
Yana ƙoƙarin samun takaddun da yake buƙata don auren Ms Cengiz.
Ta raka shi har kofar shiga ofishin jakadancin, ta yi sa'o'i fiye da 10 a wajen ginin tana jiran Khashoggi, wanda bai sake fitowa ba.
A cikin rahotonta, Ms Callamard ta kammala cewa an kashe Khashoggi a cikin karamin ofishin a ranar. Ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta saurari faifan faifan bidiyo na tattaunawa a cikin karamin ofishin jakadancin da hukumomin leken asirin Turkiyya suka yi.
Masu gabatar da kara na Saudiyya sun ce kisan da aka yi ba abu ne da aka shirya shi ba.
Sun ce jagoran jamian da aka tura domin su tattaunawa da shi shi ne ya bada umarnin kashe Khashoggi. An dorawa tawagar alhakin mayar da Khashoggi masarautar "ta hanyar lallashi" ko kuma, idan hakan ya ci tura, "da karfi".
Masu gabatar da kara sun kammala da cewa an tsare Khashoggi da karfi bayan gwagwarmaya tare da yi masa allura da ta say a fita daga cikin hayyacinsa kuma ta yi sanadin mutuwarsa.
Daga nan ne aka sassare gawarsa aka mika ga wani "abokin hadin gwiwa" a wajen ofishin jakadancin. Ba a sake ganin gawarsa ba.
Masu shigar da kara a Turkiyya sun yi ittifakin cewa an shake Khashoggi ne a lokacin da ya shiga cikin ofishin jakadancin, kuma sun kawarda gawarsa.