Yadda fasaha take taimakawa wajen magance matsalolin hanyoyin Afirka masu wahalar sha'ani

    • Marubuci, Daga Gabriella Mulligan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter, Cape Town
  • An wallafa

Benson Ndumu Mwangi ya shafe shekaru 10 yana tuka babbar mota da ke jigila a titunan kasar Kenya da ke a Gabashin Afirka.

Aiki ne mai matukar wuya: "Tukin babbar mota na da kalubale a Kenya, yawancin hanyoyin ba su da kyau, tuki na da wahala, yana janyo lalacewar mota da tsaikon isa inda kake son zuwa.

"Wasu yankunan na da hatsarin gaske da barayi, don haka dole mu yi taka-tsantsan," in ji shi.

Ga Mista Mwangi da masu irinsa matuka suna da kyakkyawan fata sabuwar yarjejeniyar kasuwanci maras shinge da aka cimma a Afirka za ta inganta yanayin aikinsu.

Yarjejeniyar kasuwanci maras shinge da aka cimma a Afirka (AfCFTA) ta shiga shekara daya da fara aiki. A shekarar 218 kasashen Afirka 54 ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Manufar ita ce bunkasa kasuwancin kayayyakin da kasashen nahiyar ke samarwa, da safararsu cikin kwanciyar hankali.

Farin farawa a shekarar 2020, za a rage harajin kashi 90, da ya bunkasa kayayyakin ba tare da zaftare kudade ba.

Bankin Duniya ya kiyasta cewa matakin zai bunkasa fita da kayayyaki tsakanin kasashen Afirka da kashi 81 zuwa shekarar 2035. Yarjejeniyar za ta bunkasa zuba jari a fannin kimiyya da fasaha tsakanin kasashen nahiyar.

Kamfanin babbar mota na Amitruck na gudanar da harkokinsa ta intanet, wanda yake da alaka da masu saye da sayarwa daga cikin manyan kamfanoni. A yanzu kamfanin na aiki da direbobin manyan motoci 6,000.

Abokan hulda za su shigar da bayanansu da inda za a kai kayan ta manhajar. Wannan ya sanya an samu rage kashe kudi ta fannin zuwa hayar mota da sauran tsarabe-tsarabe.

Ana samun kwararrun direbobi, kaya za su isa inda aka nufa cikin tsanaki, ana tanadar motocin da ke jiran ko za a samu wata matsala su maye gurbinta ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban kamfanin Amitruck, Mark Mwangi, ya ce yana ganin harkar sufuri wani fanni ne da zai bunkasa da kawo ci gaba ga Afirka.

"Kirkira da samar da hanyoyin safarar kayan da kamfanonin Afirka ke yi a tsakaninsu, zai fitar da nahiyar daga kangin bakin talaucin da ya yi mana katutru," in ji Mista Mwangi.

"Amma idan ana son yin kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, ya kamata kamfanoni su bunkasa kayan da suke yi a cikin gida."

Sauran kamfanoni na ba da zabin dakon kayan ta ruwa ko ta sama. Sai dai tsohuwar hanyar da ake amfani da ita ta dakon kayayyaki ta sama ko kasa na bukatar sai ka je wani ofishi domin shigar da bukatar hakan, ko jami'an kwastam da sauransu.

Kamfanin MVX na Najeriya na kokarin sauya hakan, ta hanyar yin komai ta intanet ciki har da bibiyar kayan daga inda suka taso har inda za a sauke.

Abaya, mai aike da kaya sai ya nemo masu dakon kayan, da zabar lokacin da za a zo a dauka, ya yi amfani da wakilin fannin sufuri, da nemo kwantena, da inda za a kai kwantenar da sauran tsarabe-tsarabe. MVX na sanya duk wadannan a shafinsa na intanet, inda kamfanoni abokan hulda ke kula da sauran shirye-shiryen daukowa da kai kayayyakin.

"Yarjejeniyar kasuwanci na hakika, ba komai ba ne matukar an inganta fannin sufuri," in ji, Tonye Membere-Otaji, shugaban kamfanin MVX.

"Wannan shi ne fannin da nahaiyar ta gaza da ake bukatar bunkasawa," in ji shi.

Ya yin da nahiyar ke cikin na biyu masu yawan al'umma, inda kashi 17 na al'ummar duniya suka fito, amma Afirka na da kashi 2 ne kacal na kasuwanci a duniya.

Sai dai duk da hakan, ana bukatar kwakkwarar kimiyya da fasarar inganta shi.

Yawanci dai ana ganin yarjjeniyar AfCFTA ba za ta yi karko ba, idan ba a samar da hanyoyi masu inganci ga kamfanonin da ke jigilar kayayyakin ba.

"Idan muka yi duba, za mu ga cewa idan ana son shugabar kamfanin sufuri ta sama da ruwa a kasar Ghana mai suna Jetstream Africa.

"Labari mai dadin shi ne gwamnatocin nahiyar sun fara zuba jari a manyan ayyukan ababen more rayuwa wadanda."

Masu zuba jari za su kara fadada girman tashar ruwan, da bayar da dama ga manyan jiragen dakon kaya na kasashen duniya zuwa tashar.

A bangare guda kuma, domin saukaka cunkoso a iyakokin kasashe misali daga Botswana zuwa Zambia, an bude wata sabuwar gada akan kogin kasar a wannan shekarar.

Har wa yau, sabbin ayyukan ababen more rayuwa, za su kara bunkasa fannin sufurin.

Da sanya doka mai tsari kan shiga da fitar kayayyaki, da biyan kudade da haraji, da yin garambawul a fannin samar da kayayyaki a cikin gida.

Najeriya ma ta na bukatar samar da wani tsari, "da zai bai wa 'yan kasuwar Afirka saukin shiga babban birnin kasar, da samun saukin baza haja tsakanin 'yan kasuwar," in ji Mista Membere-Otaji.

"Baki daya daya gwamnati na bukatar gyara fannin ta yadda 'yan kasuwa za su ji dadin gudanar da harkokinsu."

Ga direbobin manyan mota irinsu, Benson Mwangi, sauyin da ci gaban ba zai iske su cikin sauri ba.

"Da zarar ka isa iyaka, za ka tadda dogon layin motoci, wani lokacin za motar ka za ta iya zama kan layi kwana guda ko fiye da hakan," in ji shi.