Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hare-haren Uganda: Sirrin ƙungiyar ƴan tawayen ADF mai alaƙa da IS
- Marubuci, Daga Patience Atuhaire
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kampala
- An wallafa
Wani tsohon mamba a ƙungiyar Allied Democratic Forces (ADF) ya ce ƙungiyar na tsoratar da mambobinta domin daidaita al'amuran ƙunigiyar. ADF ɗin ce wadda ke da alaƙa da IS ake zargi da kai harin ƙunar baƙin-wake na baya-bayan nan a Kampala, babban birnin Uganda.
"Ana amfani da tsarin shari'a wajen tafiyar da ƙungiyar, idan ka yi sata za ka rasa hannunka. Idan ka yi fyaɗe za ka mutu. Idan ka yi ƙarya game da wani kuma aka gano ka za ka mutu," Peter, wanda aka ɓoye sunansa domin ba shi kariya ya shaida wa BBC hakan.
Yana murmushi baki ɗaya a lokacin da yake bayar da wannan labarin maimakon ya yi rawar baki - wanda hakan alama ce da ke nuna cewa ba ya cikin wata damuwa ko fargaba.
An tilasta wa matashin shiga ƙungiyar kuma ya shafe shekara biyu a matsayin ɗan bindiga, inda ya gane wa idonsa yadda aka rinƙa yanke hannuwan mutane da fille musu kai - wani lokacin ma abokansa ma aka yi wa hakan.
Tsoro da irin haka ya saka, da kuma alaƙar ƙungiyar da IS ya sa ƙungiyar ta ADF ta ƙara ƙarfi har take yi wa Uganda barazana.
Tsawon shekaru, gwamnatin Uganda ta bayyana cewa ADF ƙungiya ce da aka gama da ita, amma da alamu a yanzu ba haka lamarin yake ba.
Yawan rikice-rikice tun a watan Oktoba ciki har da harin bam biyu da aka kai a tsakiyar Kampala sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum takwas, ciki har da ƴan bindiga uku da kuma raunata sama da 40.
Tun asali an kafa ƙungiyar ADF a shekarun 1990 inda Jamil Mukulu ya kafata inda a lokacin mabiyanta ƴan Uganda ne waɗanda ransu ya ɓaci kan yadda gwamnatin ƙasar ke tafiyar da Musulmi.
An bi diddigin ƙungiyar inda aka fatattake ta daga yammacin yankin Rwenzori inda a nan ne mayaƙanta suka yi ta kai hare-hare a ƙauyuƙa da kuma ƙona makarantu a farkon shekarun 2000.
Sauran ƴan ƙungiyar sun tsallaka iyaka inda suka tafi gabashin Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo domin neman aiki.
Tun da farko, mayaƙan ADF da ke can sun yi ta aiki da al'ummar garuruwa domin yin kasuwanci, wanda hakan ya sa aka sansu a kusa da garin Beni, kamar yadda wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana a 2011.
Sai dai an samu sauyi bayan da suka soma kai hare-hare ga Kiristoci.
Yaudara ta hanyar ƙarin girma a cikin ƴan tawaye
Bayan wannan lokaci ne Peter, wanda yake zama a Uganda ya yanke shawarar zuwa Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo domin neman aiki. Wani ya shaida masa cewa za a samu kuɗi a can.
Sai daga baya ya gane asalin dalilin da ya sa aka ja shi zuwa wajen bayan wasu masu riƙe da makamai sun fito daga cikin dazuka a lokacin da yake tafiya zuwa cikin Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo inda suka umarce shi da ya bi su.
An saka wa Peter bindiga a kai inda aka dauƙe shi aikin ADF - duk da cewa a yanzu ƙungiyar na kiran kanta da Madina at Tauheed Wau Mujahedeen (MTM).
"Ban tsaya na yi tunani kan me ke faruwa ba. Mun yi amfani da hanyoyi daban-daban na sufuri ciki har da kwale-kwale kafin a isa sansanin horaswa na ƙungiyar," kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Mutum yana isa za a karanta masa dokoki: Idan ka yi ƙoƙarin guduwa za a fille maka kai, haka ma idan mutum ya ƙi yarda a horas da shi za a fille masa kai."
Peter ya bayyana cewa MTM ta yi mubaya'a ga IS a lokacin da IS ɗin ke ƙarƙashin jagorancin Abu Bakr Baghdadi.
An san shi sosai a 2014, inda ya sanar da kafa sabuwar ƙungiya a yankunan Iraƙi da Syria - inda ya jagoranci ƙungiyar har zuwa 2019 a lokacin da ya kashe kansa a yayin wani samame da soji suka kai.
"Ba ma aikata komai kamar kai hari a barikin sojoji har sai mun samu umarni daga sama," in ji Peter.
"Abin da mayaƙan suka sani kawai shi ne shugabansu ɗaya shi ne shugaban IS. Runduna ce ta ubangiji."
Yara mayaƙa mara tsoro
Ƙoƙarin guduwa abu ne mai wahala sakamakon ba abu bane mai yiwuwa mutum ya haɗa kai da wani ba tare da tunanin cewa za a kai ƙararsa ba, in ji shi.
Sai dai bayan wani lokaci, da dama daga cikinsu sun zamo suna son wannan hanya, inda suke kallon AK-47 a matsayin jininsu, kamar yadda Peter ya bayyana.
Wasu daga cikin yaran da suka sadaukar da rayuwarsu wajen yaƙin akwai yara ƴan shekara 10 zuwa 15, in ji shi.
"Su ne ke sauri wajen sa kai idan za a kai wani hari. Ba su tsoro, sakamakon sun yarda da koyarwar da aka yi musu ta zuwa aljannah. Da dama daga cikinsu ƴan Congo ne inda aka ɗauke da dama daga cikinsu daga iyayensu a lokacin da aka kai wa ƙauyukansu hare-hare," in ji shi.
Wani binciken haɗaka da ofishin kare haƙƙin bil adama na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi tsakanin Janairun 2019 zuwa Yunin 2020 ya ce an kashe farar hula 1,066 tare da ɗaukar yara 59 inda ADF suka mayar da su sojoji a lardunan Arewacin Kivu da kuma Ituri a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.
ADF ɗin ta koma wata ƙungiya da aka santa matuƙa a duniya a lokacin da Musa Bukulu ke jagorancinta, wanda wani mutum ne ɗan Uganda wanda yake shekarunsa na 40 a lokacin da ya gaji mulki.
Wanda ya gabace shi an kama shi ne a 2015 a Tanzania wadda ke makwaftaka da DR Congo da Uganda inda daga baya aka tasa ƙeyarsa zuwa Uganda a lokacin da ake masa shari'a.
"Ganin cewa Mukulu ne ya ƙirƙiro ADF, da niyyar komawa Uganda domin kafa gwamnatin Musulunci da za ta zama kishiya ga masu riƙe da makamai a faɗin duniya, Baluku ya so ya kafa ADF a matsayin wata babbar ƙungiya ta duniya," kamar yadda wani rahoto na baya-bayan nan da Jami'ar George Washington ta fitar a kan tsatsauran ra'ayi.
A wani bidiyo da aka saki a gidan talabijin na Muhajideen a bara, Baluku ya bayyana cewa: "Babu wani batun ADF da Ikon Allah, babu ADF da daɗewa.
"A halin yanzu, mun zama lardi, lardin tsakiyar Afrika, wanda lardi ne guda daga cikin larduna da dama suka kafa Islamic State."
A ƙarƙashin jagorancinsa, an bayyana cewa ƙungiyarsa ta samu kuɗi sosai daga masu ɗaukar nauyin IS.
Bugu da ƙari, tsakanin 2016 zuwa 2017, ADF ta wallafa sama da bidiyo 30 a shafukan sada zumunta inda a cikin bidiyon akwai tambarin MTM inda take cewa a yanzu tana cikin ƙungiyoyin jihadin duniya.
A lokacin da aka kai hari ga gidan fursunan Kangbayi da ke a Beni a Oktoban 2020 har aka saki sama da mutum 1,000, duka ADF da IS sun ɗauki nauyin kai hare-haren.
Baluku, wanda aka saka shi a cikin jerin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a Agustan 2020, kuma hakan ya ja hankalin mayaƙa daga yankin Great Lakes da gaban yankin.
"Babban burin ƙungiyar ba wai Uganda kaɗai bane," in ji Peter.
"Abin da suke so shi ne su mamaye duniya baki ɗaya. Akwai mayaƙan Tanzania da Kenya da Rwanda da Burundi da Somalia hgar ma da Larabawa," in ji tsohon mayaƙin.
Neman yafiya ga mayaƙa
Abin da ba a sani ba shi ne harin baya-bayan nan da aka kai na ƙunar baƙin wake wanda ya kai harin ya tsallako daga iyaka ne ko kuma an ɗauke shi a matsayin mayaƙi ko kuma an horas da shi ne kuma an ba shi makamin a Uganda.
Hukumomi sun bayyana cewa sun yi ƙoƙarin kakkaɓe ƴan ta'adda a faɗin ƙasar - tun daga Rwenzori zuwa Kampala wanda alama ce ta irin barazanar da ta faɗaɗa.
A ƙoƙarin yaƙi da ta'addanci a fadin ƙasar bayan harin da aka kai a makon da ya gabata, gwamnatin ƙasar ta kama sama da mutum 100 da kuma kashe aƙalla mutum bakwai da ake zargi.
Peter ya yi ƙoƙarin guduwa ne watanni kaɗan da suka gabata kuma gwamnatin Uganda ta yafe masa a hukumance, yana daga cikin tsofaffin mayaƙan ADF 23 da suka buƙaci a yafe musu tun a 2019.
Ya samu kuɗi ƙalilan da za su taimaka masa ya sake sabuwar rayuwa kusan dala ɗari.
Sai dai bai samu wani taimako ba na shawarwari domin gyara tunaninsa kuma ya zama abu mai wahala a gare shi ya samu aiki.