Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yakin Tigray na Ethiopia: Abiy Ahmed ya sha alwashin shiga sahun gaba a yaki da 'yan tawaye
Firaiministan Habasha, Abiy Ahmed, ya sha alwashin jagorantar yaki da 'yan tawaye, wadanda rahotanni ke cewa suna kara dannawa kusa da babban birnin kasar Addis Ababa a daidai lokacin da yaki ke kara zafafa tsakanin bangarorin biyu.
Abiy Ahmed, wanda ya samu lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiyaa shekarar 2019, ya ce wanzuwar kasar Habasha na fuskantar barazana.
Yakin da aka dauki shekara guda ana yi tsakanin gwamnati da 'yan tawayen yankin Tigray, ya janyo aikin jinkai mafi girma da kasar ta fuskanta cikin shekaru masu yawa.
Daruruwan 'yan Tigray ne ke fama da matsananciyar yunwa da fari ya sake haddasawa.
An kuma kashe dubban mutane, yayin da sama da miliyan daya suka tsere daga muhallansu.
"Daga gobe Laraba, zan jagoranci tawagar dakarunmu domin matsawa sahun gaba a yakin karbo kasarmu," in ji Mista Abiy kamar yadda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Litinin.
"Ina wadanda suke son shiga cikin tawagar 'ya'yan Habasha, da tarihi zai jinjina musu, ku taso ku kare kasarku, mu hadu a fagen daga."
Mista Abiy dai yana da mukamain Laftanar Kanar din soji ne, kuma ya shiga yakin da kasar ta yi tsakaninta da Eritrea tsakanin shekarar 1998 zuwa 2000.
Ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekarar 2019, bayan kawo karshen 'yar tsamar kusan shekaru 20 tsakanin kasar Habasha da makwabciyarta Eritrea, ta hanyar yarjejeniyar zaman lafiya.
Sanarwar da Abiy ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da su ma dakarun 'yan tawayen 'yantar da yankin Tigray suka sanar da cewa suna gab da shiga birnin Ababa.
Sai dai gwamnatin Habasha ta musanta hakan. An yada wani bangare na kalaman firaiminista na nuna kosawa da zuwa iya wuya kan abin da ke faruwa, kamar dai yadda wakilin BBC na Afirka Andrew Harding ya rawaito.
Kungiyar TPLF ta yi watsi da sanarwar Mista Abiy, kamar yadda mai magana da yawunta Getachew Reda ke cewa "dakarunmu ba za su damu da maganganun da suke yi ba, suna son tsorata mu domin janyewa, lamarin da ba zai faru ba kenan."
Kungiyar Tarayyar Afirka na kokarin ganin ta shiga tsakani domin sasanta bangarorin biyu, domin hawa teburin sulhu.
A farkon watan nan ne sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya yi gargadin cewa tashin hankalin, da abin da ya rikide ya zama yaki na barazana ga 'yan kasar da zaman lafiya yankin baki daya.
Tun da fari rashin jituwa tsakanin Firai minista Abiy da kungiyar TPLF ne ya janyo tashin hankalin, wadda ke ganin cikin shekaru 27 ana maida 'yan Tigray saniyar ware.
A shekarar 2019 ne Mista Abiya ya yi nasarar zama firaiministan kasarta Habasha, cikin kankanin lokaci ya fara sauye-sauye masu inganci, ciki har da kawo karshen rashin jituwar kusan shekaru 20 tsakanin kasar da Eritrea, kuma a wannan lokacin ba sanya ko mutum guda daga shugabannin yankin a kokarin sasantawar.
Watanni 12 da suka wuce ne aka kara samun wata jituwa tsakanin Abiy da TPLF, lamarin da daga bisani ya janyo dakarun Tigray da akai zargin sun kai hari sansanin sojin Habasha da ke yankin tare da sace makamai, inda ita kuma gwamnati ta maida zazzafan martani.
Karin labarai kan rikicin Tigray: