Abin da gwamnatin Najeriya ke fatan cimma da ziyarar Anthony Blinken

An wallafa

Yayin da Sakataren Wajen Amurka Anthony Blinken zai sauka a Abuja, babban birnin Najeriya a ci gaba da ziyarar kasashen Afirka uku a wannan Alhamis ɗin, ga alama Amurkar ta cire Najeriyar daga jerin kasashen da take zargi da tauye 'yancin addini.

Labarin cire Najeriya daga cikin ƙasashe shida wadanda a shekarar ta 2020 Amurkar ta yi musu lamba ta kasancewa wadanda suke tauye 'yancin addini labari ne da zai dadada wa hukumomin kasar.

Domin hukumomin Najeriyar za su karbi wannan babban bako nasu da faran-faran, abin da kuma ba zai yi wa masu ja da hakan ba dadi.

Babu dai wata sanarwa da ta fito ta musamman karara ta bayyana matakin daga walau Amurkar ko kuma gwamnatin Najeriya, kan abin da ya kai ga zare sunan Najeriyar daga kasashen da Amurkar take yi wa wani kallo na musamman saboda sun sa kansu ciki ko suna kau da kai ga tsagwaron keta 'yancin addinai.

Wata sanarwa ce Amurkar ta fitar ranar Laraba, wadda ke dauke da sunayen ƙasashen da Amurkar ta sa cikin kundinta na bana, 2021 na masu tauye hakkin addinai sai kawai aka ga ba sunan Najeriyar a ciki.

Sai dai ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP na masu ikirarin jihadi da ke harkoki a yankin arewa maso gabashin ƙasar sun ci gaba da kasancewa a jerin wadanda Amurkar ke nuna damuwa ta musamman a kansu.

'Muna murna da ziyarar Blinken'

Mista Blinken na ziyartar Najeriya ne daga ranar Alhamis din nan, a zango na biyu na rangadin ƙasashen Afirka uku da ya faro, cikinsu har da Kenya da Senegal.

Kakakin shugaban Najeriya, Mallam Garb Shehu, ya ce suna murna ainun da wannan ziyara kasancewar Amurkar ta ba wa Najeriyar matsayin da ya cancanceta a wannan karon, ba kamar a baya ba.

Ya ce, ''Mu abin da ya ba mu sha'awa shi ne, akwai sako na sabuwar gwamnatin Joe Biden na Amurka, sako ga daukacin al'ummar Afirka.

''Kuma aka ce Najeriya aka zaɓa don a zo a yi wannan jawabi, don a isar da shi ga al'ummar Afirka. Wannan Akwai jawabi da Mista Blinken zai gabatar.''

''Wannan manuniya ce ga irin fifiko da martaba da gwamnatin Amurka mai ci yanzu ta dora da martaba da daraja da take ganin gwamnatin Buhari a duniya baki ɗaya.

Lokacin da Obama ke mulki ai an yi irin wannan jawabi ba a neme mu ba, a Egypt aka je ak yi irin wannan jawabi,'' in ji Garba Shehu.

Batutuwan da ake fatan cimma

Ana sa ran Mista Blinken zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari don tattaunawa kan yadda ƙasashen biyu za su inganta ayyukan haɗin gwiwa a fannin kula da lafiya na duniya da tsaro da bunƙasa hanyar samun makamashi da haɓaka tattalin arziƙi.

Najeriya tana fama da barazanar tsaro mai yawa ciki har da yaƙin ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram sama da shekara goma da rikice-rikicen ƙabilanci da ɗumbin satar ɗalibai daga makarantu da gungun 'yan bindigar da ake kira 'yan fashin daji ke yi.

A lokacin da yake Abuja, Sakatare Blinken zai kuma gana da masu sana'o'i ta intanet a Najeriya.

An ayyana Najeriya cikin ƙasashen da ake ƙara tsuke sararin watayawar fararen hula saboda batutuwa kamar zaluncin 'yan sanda wanda ya harzuƙa gagarumar zanga-zanga a bara.