Shugaba Biden da takwaransa na China na ganawarsu ta farko

An wallafa

Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na China Xi Jinping sun fara ganawarsu ta keke da keke ta farko ta bidiyo.

Suna ganawar ne wadda aka sanya wa rai sosai yayin da zaman tankiya tsakanin kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki ya karu a kan batutuwan da suka shafi Taiwan da kasuwanci da kuma hakkin dan adam.

Wannan dai ita ce wata ganawa mafi tasiri da shugabannin biyu suka taba yi tun bayan da Mista Biden ya hau mulki a watan Janairu.

A yayin tattaunawar ta su bayan musayar gaisuwa da suka yi, Mista Biden ya ce nauyi ya rataya a kan kasashen biyu na su tabbatar da cewa gabarsu ba ta kai su ga rikici na fili ba.

Ya ce, "kamar yadda taba fada a baya, ina ganin nauyin da yake kanmu a matsayin shugabannin China da Amurka, shi ne mu tabbatar cewa gogayyar da take a tsakanin kasashenmu ba ta kai ga rikici ba, da niyya ko ba da niyya ba, kawai dai gogayya ta lami lafiya. Ina gnin muna bukatar mu rika aiki da hankali da natsuwa, da kuma nuna gaskiya inda muke da sabani, sannan kuma mu yi aiki tare inda muradinmu ya hadu, musamman a kan muhimman batutuwa na duniya kamar sauyin yanayi.''

Mista Biden ya kuma ce, ''Mun yi amanna, kuma kai da ni mun yi magana a kan wannan -dole ne dukkanin kasashe su bi dokokin da suka kamata, kuma abin da ya sa Amurka a ko da yaushe take tashi tsaye a kan muradunmu da kuma na kawayenmu da abokanmu.''

Wadannan kalamai na Mista Biden tamkar na amincewa da Taiwan ne- wadda wannan batu ne da kasashen biyu ke kai ruwa rana a kai.

Beijing na daukar Taiwan a matayin wani lardi na kasarta da ke neman ballewa, yayin da ita kuwa taiwan ke kllon kanta a matsayin kasa mai 'yancin kanta.

Amurka dai ba ta saurarawa a kan ganin ta kare Taiwan a ko da yaushe.

A watan da ya gabata Mista Biden ya ce Amurka za ta kare Taiwan idan China ta kai mata hari, a wani abu da ya yi kama da sauyin yanyi na manufar waje t Amurka d ak dade da sani, na kin fitowa fili karara ta bayyana ainahin abin da za ta yi.

Shi kuwa a bangarensa Shugaba Xi na China cewa ya yi kasashen biyu na bukatar inganta sadarwa a tsakaninsu kuma su fuskanci kalubale tare.

Mista Xi ya ce "Dan adam na rayuwa a wata duniya da take a dunkule wuri guda, kuma muna fuskantar kalubale da dama. Saboda hak China da Amurka na bukatar kara sadarwa da hadin kai." .

Ya kuma ce akwai bukatar samun kyakkyawar alaka ta China da Amurka domin fuskantar kalubale na duniya kamar annobar korona, kamar yadda kafar yada labarai ta gwamnatin China ta ruwaito.

Kasashen biyu masu hamayya da juna sun shammaci duniya a makon da ya gabata inda suka fitar da sanarwa ta hadin guiwa kan batun sauyin yanayi a wurin taron koli na Glasgow, Scotland.

Haka kuma daga cikin batutuwan da shugabannin biyu za su tattauna akwai, tsaro na intanet da kasuwanci da nukiliya, han bazuwar makaman kare-dangi ma na cikin batutuwan.