Kasuwar ƴan ƙwallo: Xavi na son dawo da Alcantara, Roma na neman yi wa United fancale, Pogba zai koma Madrid

An wallafa

Sabon kocin Barcelona Xavi yana son kungiyar ta sake sayen dan wasan tsakiyar Spain Thiago Alcantara, mai shekara 30, daga Liverpool. (Sport in Spanish)

Manchester United na son siyar da dan wasan tsakiyarta na Ingila Jesse Lingard kan fan miliyan 10 a watan Janairu. (Sun)

Kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino zai yi maraba da komawa gasar Premier. (Telegraph)

Barcelona na duba yiwuwar daukar aron dan wasan Chelsea da Amurka Christian Pulisic, mai shekara 23. (Sport - in Spanish)

Dan wasan bayan Manchester City da Netherlands Nathan Ake, mai shekara 26 ne babban burin sabon kocin Newcastle Eddie Howe, wanda ya taba zama kocin Ake a Bournemouth. (90 Minute)

Dan wasan Leicester City da Najeriya Wilfred Ndidi, mai shekara 24 na kan idon Real Madrid. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Har yanzu Real Madrid din na sa ido kan dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 28. (Marca - in Spanish)

Chelsea da Real Madrid za su fafata da Bayer Leverkusen kan dan wasan Jamus Florian Wirtz, mai shekara 18. (El Nacional - in Catalan)

Chelsea na shirin neman dan wasan Monaco da Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 21. (TuttoJuve)

Chelsea ta kai tayin fan miliyan 34 kan dan wasan baya na Real Madrid da Brazil Eder Militao, mai shekara 23. (El Nacional - in Catalan)

Roma na kara matsa kaimi kan Manchester United kan yarjejeniyar aro tare da zabin siyan dan wasan bayan Portugal Diogo Dalot, mai shekara 22. (Corriere dello Sport, via Football Italia)

Leeds United ta tuntubi dan wasan Arsenal da Ingila Eddie Nketiah kan komawa Elland Road. A baya dai dan wasan mai shekaru 22 ya shafe watanni shida a matsayin aro tare da Leeds kafin a sake kiransa. (Tuttomercato)

Sabon kocin Aston Villa Steven Gerrard na sha'awar dan wasan Rangers na Finland Glen Kamara, mai shekara 26. (Record)

Gerrard kuma yana son kawo dan wasan gefe na Rangers Ryan Kent mai shekaru 25 zuwa Villa. (Metro)

Dan wasan Arsenal da Ingila Folarin Balogun, mai shekara 20, ya ce a shirye yake ya bar kungiyar don samun damar rika buga wasa a zubin farko (Mirror) Manchester United na son siyar da dan wasan tsakiyarta na Ingila Jesse Lingard kan fan miliyan 10 a watan Janairu. (Sun)

Kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino zai yi maraba da komawa gasar Premier. (Telegraph)

Barcelona na duba yiwuwar daukar aron dan wasan Chelsea da Amurka Christian Pulisic, mai shekara 23. (Sport - in Spanish)

Dan wasan bayan Manchester City da Netherlands Nathan Ake, mai shekara 26 ne babban burin sabon kocin Newcastle Eddie Howe, wanda ya taba zama kocin Ake a Bournemouth. (90 Minute )