Ku San Malamanku tare da Malam Ibrahim Mustapha Malik

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Malam Ibrahim Mustapha Malik
An wallafa

Fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya Malam Ibrahim Mustapha Malik ya ce ya samu karatun addini a ƙasar Saudiyya kuma ya yi karatun boko har zuwa digiri na biyu.

Malamin ya ce yana cikin manyan almajiran Sheikh Abba Aji fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Borno.

Ya ce ya yi karatun litattafai da dama wurin malaminsa Shekih Abba aji.

"A yanzu ni nake karantar da almajiran malam da harshen Kanuri a masallacin Abba Aji," in ji shi.

Malam Ibrahim Mustapha Malik yawacin tambayoyin da aka fi yi masa sun shafi harakar aure da iyali

Malamin ya ce an haife shi ne 1955a jihar Borno.

Tun yana ɗan shekara shida aka kai shi makarantar tsangaya a garin Kusur da ke kusa da Geidam a waureren 1961.

Amma saboda fari da aka yi fama da shi a lokacin a yankin Borno aka mayar da shi gida. Ya ce a gida ya ci gaba da karatu wurin malamansa - malam Bukar da Malam Abba.

Malamin ya ce Iyayensa sun tafi shi Sudan da nufin zuwa garin Makkah a tafiyar ƙasa.

Ya ya taɓa yin wata tafiya ƙasa mai nisa daga wani gari zuwa garin Khartoum na Sudan.

Ya ce a Sudna ya koyi karatun turanci da harshen larabci.

Malamin ya ce matarsa ɗaya a yaznu kuma yana da ƴaƴa fiye da 10 da da jikoki fiye da 20.

Malamin ya ce abincin da ya fi so shi ne tuwon alkalama da dawa da miyar kuka.