Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jigawa za ta yi dokar hukunta masu yin ba-haya a fili
Majalisar dokokin jihar Jigawa a arewacin Najeriya tana nazari kan wani ƙudirin doka da zai hukunta duk wanda aka samu yana bahaya a fili.
Tun da farko ma'aikatar ruwa ta jihar ce ta aike da ƙudirin gaban majalisar a wani mataki na daƙile yin bayan-gida barkatai a sassan jihar.
Honorabul Haruna Aliyu Dangyatin shi ne shugaban kwamitin harkokin ruwa na majalisar dokokin jihar kuma a tattaunawarsa da BBC ya ce an yi wa kudirin dokar karatu na daya da na biyu.
Ya kuma ce ƙudirin ya ƙunshi abubuwan da dama, "na farko a nuna wa mutum muhimmancin cewa shi ba dabba ba ne, bai kamata ya yi ba haya a ko ina barkatai ba," a cewarsa.
Abu na biyu shi ne kudurin ya ƙunshi cewa idan ka yi ba-haya akwai tara da za a yi maka.
"Ya danganta, akwai wanda za ka biya tarar kudi kawai, akwai wanda za a sa ka aiki sannan kuma ka biya tarar, ko kuma a kai ka gidan gyaran hali kuma ka biya tara, saboda muhimmancin lafiya da kuma al'umma."
Ya ce zuwa yanzu ba a yanke ko nawa za a dinga karɓar tarar ba sannan ɗaurin ma ba a kai ga yanke tsawonsa ba.
"Abu ne da yake gaban kwamiti sai ya gama tsarawa tukunna, sannan sai mu kai gaban majalisa, idan sun amince da tsarin da muka yi to daga nan ne za mu faɗi adadin tarar da kuma tsawon zaman.
"Don haka yanzu ba zan iya cewa komai a kai ba kar ya zama ra'ayin kaina na faɗa," in ji Honorabul Dangyatin.
Ya ƙara da cewa a yanzu an kai gaɓar bita dangane da wannan ƙuduri. "Ba don wasu harkoki na kasafi ba ma da tuni mun yi bitar, daga nan kuma za mu yi zaman jin ra'ayin jama'a a majalisa sannan mu gabatar da shi ga zauren majalisar.
Ana sa ran za a ƙarƙare dukkan wannan batu kafin ƙarshen shekarar nan in ji ɗan majalisar.
A duk lokacin da aka sanya irin wdannan dokoki masu alaƙa da tsaftar muhalli ba a rasa abubuwan da ake son cimma, don haka ne Honorabul Dangyatin ya ce su ma suna son yin wannan dfoka ne don ganin cewa mutanen jihar Jigawa suna cikin ƙoshin lafiya.
"Sannan a ce mutanen Jigawa masu tsafta ne da kula da lafiyarsu da ta iyalansu, a daina kashi barkatai kawai idan za ka yi ba-haya ka san inda ya kamata ka je ka yi don rage cututtuka," kamar yadda ya ƙara da cewa.
Kafin majalisar dokoki ta fara wannan kuduri dai ita ma majalisar zartarwar jihar tana shirya nata, sannan ya ce Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef ma yana taimakawa sosai a irin wannan tafiyar.
A yanzu haka akwai ƙananan hukumomi 18 a jihar Jigawa da Unicef ta ayyana su a matsayin waɗanda ba a yin kashi barkatai.
Daga cikin ayyukan da Unicef ke yi har da taimakawa wajen tona shadda don amfanin mutane.