Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Pogba, Messi, Sterling, Cavani, Werner, Ramsey
Paul Pogba na son ci gaba da zama a Manchester United, amma sai idan kungiyar za ta kara masa yawan albashi ya wuce Cristiano Ronaldo inda zai zamo dan wasan da ya fi daukar albashi mai yawa a gasar Premier. (L'Equipe, daga Metro)
Barcelona na shirin kara karfin gabanta a watan Janairu, inda take duba yuwuwar sayen 'yan wasan da suka hada da Raheem Sterling na Manchester City da Ingila da Edinson Cavani na Manchester United da Uruguay da kuma dan Jamus Timo Werner na Chelsea. (Marca daga Mirror)
Haka kuma alamu na nuna cewa Lionel Messi, zai iya komawa Barcelona duk da cewa gwarzon dan wasan na duniya sau hudu, wata uku da ya wuce kawai ya bar Barca ya koma Paris St-Germain. (Daily Star)
Aston Villa za ta biya Rangers kusan fam miliyan uku na diyya idan Steven Gerrard ya zama sabon kociyanta. (Times)
Newcastle na duba yuwuwar sayen dan wasan tsakiya na Faransa Adrien Rabiot, mai shekara 26, daga Juventus a watan Janairu. (Calciomercato daga Mirror)
Sai dai kuma a Ingila Newcastle din ka iya gamuwa da kalubale na saye ko aron 'yan wasa daga kungiyoyin Premier a watan Janairu saboda manyan kungiyoyi ba sa son sakar mata 'yan wasa. (Telegraph)
Liverpool na nazarin 'yan wasan da za ta dauka guda uku a watan Janairu domin maye gurbin Mohamed Salah da Sadio Mane da Naby Keita lokacin da 'yan wasan uku za su tafi buga wa kasashensu gasar cin Kofin Afirka. Dan wasan tsakiya na Inter Milan Marcelo Brozovic, dan Crotia mai shekara 28, na daga cikin wadanda kungiyar ke dubawa. (Daily Star)
Babban dillalin 'yan wasa Jorge Mendes na kokarin shawo kan matashin dan wasan tsakiya na Fulham da ke taka wa Ingila leda Fabio Carvalho mai shekara 19, kan ya yard ya koma Liverpool. (Daily Mail)
Har yanzu dan wasan gaba na Fiorentina Dusan Vlahovic, shi ne Juventus, ta fi son saye duk da cewa kungiyoyin Premier sun kwallaf ransu a kan dan wasn na Serbia mai shekara 21. (Tuttosport )
Masu yi wa Bayern Munich farautar 'yan wasa sun sa ido a kan matashin dan wasan gaba na West Brom Reyes Cleary, mai shekara 17, wanda ya ci kwallo 14 a wasa 12 a bana. (Daily Mail)
Dan bayan Denmark Andreas Christensen, mai shekara 25, ya gaya wa magoya bayan Chelsea cewa kada su damu da makomarsa duk da cewa kwantiraginsa zai kare a bazara. (Standard)
Ci gaba da zaman Christensen a Stamford Bridge ya dogara ne kan yadda za a kawo karshen takaddamar da ke tattare da sharudda da tsawon lokacin da sabon kwantiragin da kungiyar ta gabatar masa ne. (Telegraph)
Juventus ta yi tayin ba wa Roma aron dan wasan tsakiya na Wales Aaron Ramsey, mai shekara 30. (Calciomercatio)