Hotunan da suka lashe gasa kan muhalli ta 2021
Mai daukar hoto dan kasar Sifaniya Antonio Aragón Renuncio ya lashe gasar hotuna kan muhalli ta shekarar 2021 kan hoton da ya dauka yana nuna wani karamin yaro yana bacci a cikin wani gida da zaizayar kasa ta rusa a gabar tekun Afiadenyigba da ke Ghana.

Asalin hoton, Antonio Aragon Renuncio
Hoton, wanda aka yi wa lakabi da The Rising Tide Sons, ya nuna yadda koguna suke kara cika a kasashen Yammacin Afrika, lamarin da ke tilasta wa dubban mutane barin gidajensu.
Renuncio ya samu kyautar £10,000.
Gasar Hotuna kan Muhalli ta Shekara, wadda aka shafe shekara 14 ana yi, ta nuna wasu daga cikin hotuna masu kayatarwa kan muhalli.
Gasar tana fito da yadda dan adam yake kokarin rayuwa sannan tana bayar da goyon baya a kan kiran da Majalisar Dinkin Duniya take yi wajen ganin an tabbatar da muradun karni kan muhalli.
An bayyana sunayen wadanda suka lashe gasar ta bana ne a wurin taro kan sauyin yanayi da ake yi a Glasgow.
Ga wasu daga cikin hotunan da suka yi nasara a gasar, da kuma bayani a kansu daga mutane da suka dauke su.

Rukunin kananan yara masu daukar hoto kan muhalli: Hoton wutar daji ne ya yi nasara a wannan rukuni. Amaan Ali ne ya dauki hoton a yankin Yamuna Ghat da ke New Delhi, Indiya.

Asalin hoton, Amaan Ali
"Wani yaro yana kokarin kashe wutar daji a kusa da gidansu da ke Yamuna Ghat, New Delhi, India."

Kyauta kan Jajircewa:Ashraful Islam ne ya dauki hoton a Noakhali da ke kasar Bangladesh

Asalin hoton, Ashraful Islam
"Garken tumaki a yayin da suke neman ciyawa a wurin da ruwa ya ƙafe.
"Fari mai tsanani a Bangladesh ya jawo rayuwa mai ƙunci ga duk wani mai rai."

Wanda ya lashe kyauta kan ci gaban birane - Hoton da Simone Tramonte ya ɗauka a Iceland na Photobioreactor

Asalin hoton, Simone Tramonte
"Na'urar photobioreactor a ɗakin gajin Alalif da ke Rykjanesbaer a Iceland na samar da da sinadarin astaxanthin."
"Iceland ta karkat daga amfai da makamashi na al'ada zuwa amfani da lantarki da kuma zafi dag makamashin da ake sabuntawa."

Kevin Ochieng Onyango ya lashe kyauta kan sauyin yanayi nawani yaro da ya ɗauka a Nairobi

Asalin hoton, Kevin Ochieng Onyango
"Wani yaro kenan ke shaƙar iska daga tsirrai tare da guguwa na tashi a bayansa a wani nuni da yake yi na irin sauyin da ke tafe."

Wanda ya lashe kyautar ruwa da tsaro: Hoton da Sandipani Chattopadhyay ya ɗauka a kogin Damodar da ke yammacin Bengal na Indiya

Asalin hoton, Sandipani Chattopadhyay
"Rashin tayuwar damina da kuma fari ya jawo gamsa-kuka ta mamaye kogin Damodar da ke Indiya.
"Gamsa-kukar na hana rana daga shiga cikin ruwa wanda hakan ke hana hallitun da ke ciki samun iskar shaƙa, kuma hakan na illa ga mutanen da ke zaune a wurin."

Wanda ya lashe kyauta kan muhallin da za a koma amfani a nan gaba shi ne Michele Lapini kuma an ɗauki hoton a kogin Panaro da ke Moderna a Italy.

Asalin hoton, Michele Lapini
"Wani gida kenan da ambaliyar ruwa ya shanye a Kogin Panaro sakamakon ruwa mai ƙarfi da kuma ƙanƙara mai narkewa."

Ga wasu daga cikin hotunan da suk cancanci yabo a gasar.
Kamun kifi a kogi, hoton da Ashraful Islam wanda aka ɗauka a Sirajgong da ke Bangladesh

Asalin hoton, Ashraful Islam
"Gamsa kuka ta mamaye ruwa kuma masu kwale-kwale na zuwa wurin kamun kifi.
"Kogin na cike da tsirai."

Hoton busar da turare, daga Azim Khan Ronnie wanda aka ɗauka a Hanoi da ke Vietnam

Asalin hoton, Azim Khan Ronnie
"Mutanen ƙasar Vietnam ne a zaune inda suke zagaye da dubban tsinkayen turaruka a ƙauyen Quang Phu Cau da ke Hanoi inda an shafe ɗarurwan shekaru ana samar da irin waɗannan tsinkayen a ƙauyen.
"Turaren na taka muhimmiyar rawa a addinin mutanen Vietnam."

Hoton wani zakin ruwa da Celia Kujala ta ɗauka a kua da tsibirin Coronado, Baja California, Mexico

Asalin hoton, Celia Kujala
"Na gamu da wannan zakin ruwan a tekun California tare da fatsa a bakinsa.
"Lokacin da na ɗauka yayin nutson da na yi, ya tsaya a kusa da ni kuma da alama yana neman taimako ne."

Hoton Lambun Nemo da Giacomo d'Orlando ya ɗauka a Noli da ke Italiya

Asalin hoton, Giacomo d`Orlando
"Lambun Nemo na wakiltar wata hanya ta noma musamman a wasu wuraren da matsalar muhalli ke sa tsirrai ba su girma da kyau.
"Wannan aikin na ƙoƙarin ganin an samu gona ta ƙarƙashin ruwa domin shawo kan matsalar sauyin yanayin da ke tafe."

Hoton yadda robobi suka cika muhalli wanda Subrata Dey ya ɗauka a Chittagong da ke Bangladesh

Asalin hoton, Subrata Dey
"Na ɗauki wannan hoton a wani kamfanin da ke sabunta roba a Chittagong da ke Bangladesh.
"Sabunta roba na taimakawa wajen kare muhalli daga gurɓata."


Asalin hoton, Pedro de Oliveira Simões Esteves
"Turakun samar da lantarki daf da fitowar rana a wani yanayi na hadari."

Dukan hotunan n da haƙƙin mallaka









