Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makabartu: Matan da ke gyaran makabartu a Kano
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Kano
- An wallafa
Mutane za su yi mamaki a ce mata na gyaran makabartu.
Ba abin mamaki ba ne domin akwai wasu mata a wata unguwa a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya da ke wannan aiki.
"Muna fada wa maza su nome ciyawar da ke makabartu amma ba ma samun wani sakamako daga gare su, shi ya sa muka yanke shawarar cewa bari mu yi aikin da kanmu," a cewarsu.
Hajiya Raliya Yahaya, ita ce shugabar kungiyar matan mai suna Kungiyar mata Musulmi, ta shaida wa BBC Pidgin cewa sun shafe sa'a huɗu suna gyaran makabartar Wailari a karshen mako.
"A karshen rana mutane za a iya binne kowa a makabartar nan kuma kowa zai ji dadin shiga ba tare da fargabar wani abu ba saboda mun gyara," in ji matan.
Matan da suka kai 10, sun shafe watanni suna aiki, suna amfani da ranakun Asabar da Lahadi daga karfe 7 zuwa 11 na safe don gyaran makabartu.
Ta yaya suka fara?
Matan sun fara wannan aiki ne lokacin da mijin Hajiya Raliya ya rasu. Shekaru bayan rasuwarsa, sai ta tara matan aure sannan ta nemi izini daga mazajensu domin su fita su fara aikin gyaran makabartu.
"Bayan mutuwar mijina, na hada matan aure tara wadanda mazajensu suka ba su izinin fita su yi wannan aiki, sannan wasu matan sun yi sha'awar shiga su yi aikin amma mazajensu suka hana," in ji Raliya.
"A duk mako idan muna wannan aiki, muna samun mazan da ke zuwa suna kallonmu, daga baya sukan shigo su dan taya mu kafin su tafi."
TA ce mazan kan zo kallonsu har ma wasu su ce "lallai wadannan mata na jin dadi wannan aiki da suke, don haka su ladansu na wajen Allah".
Dangane da kayan aikin da suke amfani da su, shugabar kungiyar matan ta ce suna arowa ne daga wajen matan da mazajensu manoma ne.
Ta ce: "Babban kalubalen da ake fuskanta shi ne babu katanga a makabartu, abin da ke janyo dabbobi na shiga suna tona kaburbura. Misali akwai wata ranar Asabar, mun bata lokaci wajen kwashe gashin jaki a wata makabarta".
Wakilin BBC Pidgin Mansur Abubakar, ya tambayi Hajiya Raliya ba sa jin tsoro idan sun kwanta barci za su yi wani mafarki na tsoro saboda sun yi aiki a makabarta?
Ta amsa da cewa: "Tun kafin mu fara wannan aiki sai dana fadawa matan idan akwai wadda take jin tsoro, to kada ma ta fara wannan aiki, saboda na san ba kowa bane zai iya aiki a inda ake binne mutane".
To amma ta ce babban dalilin da ya sa suke wannan aiki saboda maza sun gaza.
Ta ce," Ko a yau mazan suka amince da bukatarmu ta su je su rinka gyaran makabarta, to mu kuwa za mu kyale su, su yi aikin mu kuma mu koma gida mu ci gaba da kula da yara".