Kasuwar 'yan kwallon kafa: Makomar Pogba, Haaland, Hazard, Kessie, De Vrij, Brozovic, Martinez

An wallafa

Paul Pogba ya fi son ya koma inda ya fito Juventus a kan ya je Paris St-Germain ko Real Madrid a karshen zamansa da Machester United, a kaka mai zuwa lokacin da dan wasan na tsakiya mai shekara 28 zai kasance ba shi da wani kwantiragi a kansa. (Gazzetta dello Sport )

A karshe dai Erling Braut Haaland ya yanke shawarar barin Borussia Dortmund kuma wakilin dan wasan na Norway mai shekara, 21, ya fi son ya tafi Barcelona. (El Nacional)

Sai dai kuma Borussia Dortmund, na da kwarin guiwar cewa za ta shawo kan tauraron dan wasan da Manchester City da Chelsea ke hari ya ci gaba da zama, duk da cewa akwai damar sayensa ga duk kungiyar da ta biya fam miliyan 64 na na-gani-ina-so, bayan kuma farashin da za a sanya na sayensa daban, kamar yadda yarjejeniyarsa da kungiyar ta Jamus ta tanada, damar da za ta samu a shekara mai zuwa. (Manchester Evening News)

Dan wasan gaba na Real Madrid Eden Hazard zai iya tafiya Newcastle a lokacin kasuwar ƴan kwallo ta watan Janairun, kuma kociyan kungiyar ta La Liga Carlo Ancelotti a shirye yake ya bar shi ya tafi. (Star)

Antonio Conte na shirin sa dan wasan tsakiya na AC Milan dan Ivory Coast Franck Kessie mai shekara 24 zama dan wasansa na farko da zai saya a matsayin sabon kociyan Tottenham. (Metro)

Haka kuma Conte yana son Tottenham ta sayo dan bayan Inter Milan, dan Holland Stefan de Vrij, mai shekara 29, a watan Janairu. (Football Insider)

Newcastle na shirin dauke dan wasan tsakiya na Inter Milan Marcelo Brozovic inda dan Croatia mai shekara 28, zai kasance ba shi da kungiya a bazara. (Sun)

Duk da cewa Unai Emery ne ke kan gaba wajen neman zama sabon kociyan Newcastle, kociyan kungiyar na rikon-kwarya Graeme Jones, wanda a baya mataimakin Martrinez ne a aikin Belgium na neman tura kociyan na Belgium Roberto Martinez. (Football Insider)

Tottenham, West Ham da Southampton dukkanninsu na zawarcin mai tsaron ragar West Brom da Ingila Sam Johnstone, mai shekara 28, wanda kwantiraginsa zai kare da bazara. (Sky Sports)

Ita ma Tottenham na shirin yin gogayya da Juventus a kan dan wasan gaba na Fiorentina, dan Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 21. (Calciomercato)

Christian Eriksen na da damar sake komawa Ajax a watan Janairu saboda tun da dan Denmark din ya koma Inter Milan bai iya yin wasa ba saboda an sa masa wata na'ura a zuciya. (Corriere dello Sport)

Matashin dan wasan Ingila Fabio Carvalho wanda ya ki amincewa da gwaggwaban kwantiragi a Fulham, kuma dan Shekara 19 da ake alakantawa da Real Madrid, zai kasance ba kwantiragi a kansa a karshen kaka. (Sun)