Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu biyar kan wasan Bayern Munich da Benfica a Champions League
Ranar Talata Bayern Munich za ta karbi bakuncin Benfica a wasa na hudu a cikin rukuni na biyar karawa ta biyu a Champions League a tsakaninsu a bana.
Ga jerin abu biyar da ya kamata ku sani kan karawar:
1. Kakar farko da Bayern ta yi namijin kwazo
Bayern ta hada maki tara da cin kwallo 12 ba tare da an zura mata ko daya ba, ita ce kakar da Bayern ta sa kwazo a Champions League, bayan karawa uku a cikin rukunin.
2. Har yanzu Benfica ba ta taba cin Bayern ba a karawa 11
Kungiyar Jamus ta kara da ta Portugal ssau 11 a dukkan fafatawa, inda Bayern ta ci takwas da canjars uku ta kuma zura kwallo 30 a raga a fafatawar.
3. Bayern ta yi wasa 25 a cikin rukuni ba tare da rashin nasara ba
Bayern ta yi wasa 25 a cikin rukuni ba tare da an doke ta ba a Champions League ta ci 22 da canjaras uku. Wannan ne namijin kokarin da ta yi tun bayan da aka sauya fasalin gasar a 2003/04.
A filinta na Allianz ta yi karawa 22 tun daga kakar 2014/15 ba tare da an doke Bayern Munich ba, wadda ta yi nasara a wasa 21 da canjaras daya.
4. Lewandowski da kuma Muller za su kara kafa tarihi
Robert Lewandowski zai buga wasa na 100 a Champions League idan aka saka shi karawa da Benfica. Kawo yanzu ya ci kwallo 78 shine kan gaba mai yawan kwallaye a raga a gasar a jerin wadanda suka yi wasa 100.
Thomas Müller yana da kwallo 49 a Champions League, saura daya ya yi kan-kan-kan da Thierry Henry a mataki na bakwai a jerin wadanda suka ci kwallaye da yawa a gasar ta Champions League.
5. Benfica ta yi wasa shida a waje ba ta yi nasara ba a Champions League
Benfica ta buga karawa shida a waje a Champions League ba tare da yin nasara ba da yin canjaras biyu da shan kashi a wasa hudu tun bayan da ta doke AEK Athens 3-2 a Girka cikin watan Oktoban 2018.
Kuma nasarar da ta samu kenan a karawa 12 da ta yi a waje a gasar da yin canjaras uku da rashin nasara takwas.
Wadanda ke kan gaba a buga wasa sama da 100 a Champions League:
1. Cristiano Ronaldo ya buga wasa 179 a Manchester United da Real Madrid da kuma Juventus
2. Iker Casillas ya buga karawa 177 a Real Madrid da kuma Porto
3. Lionel Messi ya fafata a wasa 152 a Barcelona da kuma Paris Saint-Germain
Sauran da ke kan gaba a yawan buga Champions League:
Xavi Hernández wasa 151
Raúl González wasa 142
Ryan Giggs wwasa 141
Karim Benzema wasa 133
Andrés Iniesta wasa 130
Sergio Ramos wasa 129
Thomas Müller wasa 127
Clarence Seedorf wasa 125
Paul Scholes wasa 124
Gianluigi Buffon wasa 124