Me ya sa Turkiyya ke korar 'yan Syria kan yi wa ayaba ba'a?

A bunch of bananas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan Syria da dama na fuskantar kora daga Turkiyya bayan da suka wallafa bidiyon da ya nuna suna cin ayaba
    • Marubuci, Daga Dima Babilie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Dariya da barkwanci ta kyamara, 'yan kasar Syria sun shiga cikin sabon salo da ya bullo a shafukan sada zumunta a Turkiyya.

A cikin bidiyon TikTok na barkwanci, sun kasance suna cin ayaba suna ƙalubalantar abokansu su ma su yi hakan.

Da alama bidiyon ba shi da wata matsala a bisa tsarin TikTok na baya-baya nan. Amma yayin duk wani sabon salo ba ya daukar tsawon lokaci kafin a samu wani da ya sha gabansa , wadannan bidiyon za su iya haifar da mummunan sakamako ga wasu 'yan Syria.

A cikin 'yan kwanakin nan hukumomin kasar Turkiyya sun zargi 'yan kasar Syria da "ruruta kiyayya" saboda cin ayaba domin takalar fadan 'yan kasar. An kama 'yan Syria da dama kuma za a tasa keyarsu gida.

A wani yanayi da ake samun karuwa a tsangwamar da ake nuna wa al'ummar Syria da ke Turkiyya, ayaba ta zama alamar rarrabuwar kawuna.

To, mene ne labarin bidiyon na ayaba?

'Ayaba ta fi karfi na'

Kalubalen ayaba ya samo asali ne daga wani hoton bidiyo da ya bayyana a shafukan sada zumunta a kan zazzafar tattaunawa tsakanin Siriyawa da Turkawa kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Tattalin arzikin kasar Turkiyya ya fuskanci koma-baya sakamakon hauhawar farashin kayayyaki wanda ya jefa al'ummar kasar cikin kunci.

A cikin bidiyon, an yi musayar ra'ayoyi masu karo da juna, kuma wata budurwa 'yar kasar Syria, mai magana da harshen Turkanci, ta kare kai'dojin aikin 'yan gudun hijira. A martanin da suka mayar, Turkawa da ke cike da takaici sun ce 'yan Syria da Afganistan suna kwace ayyukansu.

Irin wannan ra'ayi dai ba bakon abu ba ne a kasar Turkiyya mai dauke da mafi yawan 'yan gudun hijira a duniya, ciki har da 'yan Syria miliyan 3.6. Ana ci gaba da nuna kyamar 'yan gudun hijira, inda wasu 'yan siyasar kasar Turkiyya masu kishin kasa ke fafutukar ganin an tsaurara matakan da suka shafi 'yan gudun hijira.

Sai dai abin da ya sa wannan hoton bidiyon ya ja hankalin ma'abota shafukan sada zumunta , shi ne abin da wani dan kasar Turkiyya ya ce: "Na ga 'yan kasar Syria a cikin wata kasuwa suna sayen kilo-kilo na ayaba, ni kaina ba zan iya saya ba."

Wani dam Siriya mai sayar da ayaba a Gaziantep

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bidiyon na 'yan Siriya da ke cin ayaba ya ba wasu Turkawa haushi

Wannan ikirari, wanda ya janyo muhawara tsakanin al'ummar Syria a Turkiyya, cikin sauri ya rikide zuwa wani sauti na bidiyo a TikTok. Domin su yi wa Baturke ba'a, Siriyawa sun yi fim ɗin suna cin ayaba.

Yayin da manufar barkwancin ayaba ita ce nishandantar da ma'abotan shafukan sada zumunta amma ba su yi wa kowa dadi ba.

Wani hoto da ya maye gurbin tutar Turkiyya da ayaba ya janyo fushin 'yan kasar. Sabuwar jam'iyyar Victory ta 'yan kishin kasa ta fitar da koke kan masu amfani da TikTok na Syria saboda "cin mutuncin al'ummar Turkiyya da tutarsu".

Wasu masu suka a shafukan sada zumunta sun ce bidiyon na "ba'a ga mummunan koma-bayan tattalin arzikin da Turkiyya ke fuskanta."

A lokacin da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki, da alama bidiyon ayaba ya harzuka hukumomin Turkiyya.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

1px transparent line

A ranar Alhamis din da ta gabata, kafafen yada labarai na cikin gida sun ce 'yan sandan Turkiyya sun kama wasu 'yan kasar Syria 11 da suka wallafa bidiyon ayaba, inda suka zarge su da " tsokana da kuma ruruta kiyayya."

Hukumar Kula da kaura ta Turkiyya ta ce za ta "kore su bayan an kammala tantance takardunsu ".

Babban Daraktan Kula da Hijira ta Turkiyya ya ce ana kokarin "gano hotunan bidiyon da aka wallafa na tsokana "tare da daukar mataki a kan dukkan mutanen da suka shiga wannan gangami".

Sai kuma a ranar Lahadin da ta gabata, hukumomin Turkiyya sun kama wani dan jarida dan kasar Syria Majed Shamaa, wanda ya yi wani rahoto a gidan talabijin kan ce-ce-ku-cen da ake yi tsakanin yan Syria da Turkawa a kan ayaba a Istanbul.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

1px transparent line

'Ba ba'a muke yi wa 'yan kasar Turkiyya ba'

Alamu sun nuna cewa wasu Turkawa 'yan siyasa sun goyi bayan kamen. A wani sakon Twitter, Ilay Aksoy na jam'iyyar Good Party mai kishin kasa ya ce ''masu cin ayaba suna yi mana ba'a suna zagin tutarmu".

Sai dai jam'iyyar Peoples Party mai goyon bayan kabilu marasa rinjaye ta ce ''wariyar launin fata ne".

A shafukan sada zumunta, 'mambobin yan Syria da ke zama a Turkiyya sun yi kokarin yin bayani a kan manufar bidiyon ayaban. Wani ya rubuta cewa; Ba da Turkawa muke yi ba, mu na yin ba'a ne ga wariyar launin fata. Durkushewar tattalin arzikin ta ya shafe mu duka."

'Yar jaridar Syria Deema Shullar, wacce ke zaune a Istanbul, ta shaida wa BBC cewa yawancin bidiyo ba su da illa kuma "barkwanci ne kawai".

Amma ta ce wasu daga cikinsu ana iya daukarsu "masu lahani ne kuma za su ba wasu haushi ". A kasar Turkiyya akwai tsauraran dokoki da suka haramta cin mutuncin kasar, tutar kasar da shugaban kasar.

Ana iya gurfanar da wadanda suka yi wadannan bidiyon ayaba a karkashin wadannan dokoki, in ji Ms Shullar.

Ta ce da yawa daga cikin 'yan Syria na fargabar tasa keyarsu zuwa kasarsu ta haihuwa, wadda ta shafe shekaru goma tana fama da yakin basasa.

Ms Shullar ta ce "laifukan a bayyane su ke ." Ta ce za a iya korar dan kasar Syria "ta hanyar sakon da ya wallafa a shafin Facebook wanda aka fassara shi ta wata hanya".

Ta ce korar ta gwamnatin Turkiyya ba komai ne illa tsoratarwa.

Ta ce hotunan ayaba sun karkata hankalin mutane daga matsalolin 'yan gudun hijira da na tattalin arziki a Turkiyya, a madadin haka, kowa ya "mayar da hankali kan bidiyon TikTok".

line