Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana ci gaba da nema masu sauran numfashi a benen da ya ruguje a Lagos
Ma'aikatan ceto sun yi aiki cikin dare domin neman masu sauran numfashi bayan da wani bene mai hawa 22 ya ruguje a Lagos yayin da ake aikin gininsa.
Kawo yanzu an gano mutum15 daga baraguzan ginin kuma daga cikinsu shida sun mutu yayin da tara suke jikkata.
An tura da motar da ke kwashe baraguzai zuwa wurin da al'amarin ya faru kuma masu aikin ceto da wasu mazauna yankin na neman masu sauran numfashin karkashin baraguzai da karafa.
Ya zuwa yanzu an gano mutun hudu masu sauran numfashi .
Tun da farko hotona daga wurin sun nuna cunkoson jama'a kusa da babban tulin takarcen.
Ba a fayyace abin da ya janyo rugujewar ginin ba da kuma adadin mutanen da suka makale a karkashin baraguzan ginin.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan rugujewar bene kuma ta yi alkawarin bayyana rahoton ga jama'a.
Mai ba shugaban kasa shawara na musaman kan harkokin manema labarai Femi Adesina, ya ce shugaban "yana jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu."
Ya kuma kara da cewa Shugaba Buhari ya umarci hukumomi da su kara kaimi wajen ceto wadanda suka makale.
Benen ya rufta ne da misalin karfe 2:45 na rana a unguwar Ikoyi ta masu ido da kwalli.
Kamfanin Fourscore ne yake gudanar da aikin ginin wanda ke da tarin ayyuka a Birtaniya da Amurka da Afrika ta Kudu da kuma wasu sassan Najeriya.
Wani ma'aikacin ginin Eric Tetteh, mai shekara 41, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa tawagarsa sun dade suna jiran wani injin tona kasa ya isa wurin lokacin da ginin ya rufta.
"Ni da dan uwana mun tsere, amma akwai mutane a ciki - mutun fiye da 100," in ji shi .
Wani ganau wanda yake aiki a ofis na wani ginin da ke kusa da wanda ya ruguje ya shaida wa BBC cewa ya ji kara, ya leka ta tagarsa kuma ya ga ginin yana gangarowa kasa.
Sai dai a cewar kamfanin dillancin labarai na AP, mataimakin gwamnan jihar Lagos Femi Hamzat ya gana da mutanen da suka fusata wadanda ke zargin mahukunta da kin fara aikin ceto cikin gaggawa.
An samu rugujewar gine-gine da dama a Lagos a 'yan shekaru nan.
A shekarar 2019, mutum 10 ne suka mutu bayan da wata makaranta ta ruguje a jihar.
A 2014, wani bena mai hawa 6 ya rufta lokacin da wani mashahuran mai yin bushara da magoya bayansa suke ibada, inda mutum 116 suka rasa rayukansu.
Sau da yawa ana sukar ka'idojin gine-gine kuma a baya baya nan hukumomin jihar Lagos sun kaddamar da wani sabon tsari na inganta takardun shaida.