Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sauyin yanayi: Firaminista Boris Johnson ya gargadi duniya
Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yi gargadin cewa muddin taron shugabannin duniya na tattauna batun sauyin yanayi a Glasgow, ya kasa cimma nasara to komai zai wargaje.
Mista Johnson ya ce babu wani dalili da zai sa a jinkirta daukar matakan takaita matsalar ta sauyin yanayin.
Firaministan na Birtaniya wanda ke wannan magana a yayin wata hira da manema labarai a daidai lokacin da shugabannin duniya ke kan hanyar bude taron mako biyu na Majalisar Dinkin Duniya kan matsalar dumamar yanayi a Glasgow, babban birnin Scotland, ya ce yadda al'amura suke na wannan matsala babu wani sauran lokaci da ya wuce yanzu da kowa da kowa zai bayar da tasa gudummawa.
Ya ce buri ko aniyar tabbatar da takaita karuwar dumamar yanayi da maki daya da rabi a ma'aunin Celcius na kafin bunkasar masana'natu na cikin wani yanayi na kila-wa-kala
Mista Johnson ya ce tuni duniya tana gani karara irin illar da sauyin yanayi ke haddasawa.
Christiana Figueres, wadda ta kasance jigo wajen samar da yarjejeniyar Paris ta 2015, yarjejeniyar da ta samar da tsarin da za a bi na wannan taron kolin na Glasgow, a hirarta da BBC ta ce kasashe na bukatar sun nuna da gaske suke wajen tashi tsaye domin cimma buri da muradun da ke kunshe cikin yarjejeniyar ta Paris;
Wannan abu ne da muke bukata mu ci gaba da ingantawa kuma mu rage yawan hayakin da ake fitarwa, har sai mun kai ga matakin da ba shi da hadari.
Jumullar dukkanin kokarin da za a gabatar, dole ne ya kasance, matuka, matuka sama da yada yake shekara biyar ko shida da ta gabata a karkashin yarjejemiyar Paris
Kuma, akwai bukatar ta kasance ta kai kusa, kusa da kololuwar da ake bukata ta yawan yanayin zafin da ake son a cimma wato lamba daya da rabi a ma'aunin celcius, wanda shi ne iya matakin da kimiyya ta ce za mu iya kai wa a wannan duniya.
Ta ce to tun da mun san cewa ba za mu iya tabbatar da cimma wannan mataki ba na daya da rabi a karshen taron na Majalisar Dinkin Duniya na sauyin yanayi na Glasgow, ai kasance dole gwmnatoci su zo su zauna nan da 'yan shekarun da ke tafe, domin su rage wannan gibi.
Tun da farko ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya nuna rashin gamsuwarsa kan yadda za a ce dole wata kasa ta rage yawan hayakin da take fitarwa mai gurbata yanayi zuwa kusan gaba daya in banda abin da ba a rasa ba, nan da shekara ta 2050.
Inda ya kafe cewa kasarsa Rasha sai zuwa shekara ta 2060 za ta iya yin hakan.