Mubi: Shekaru bakwai bayan mamayar Boko Harama

An wallafa

A ranar Juma'a 29 ga watan Oktoban 2021 ne aka cika shekaru 7 cif da mayakan kungiyar Boko Haram suka kama birni mafi girma da ya taba zaman karkashin rikonsu arewa maso gabashin Najeriya.

A ranar 29 ga wata Oktoban 2014 mayakan Boko Haram suka karbe iko da garin Mubi; birni na biyu mafi girma a jihar Adamawa.

Kodayake birnin na Mubi ya dawo cikin hayyacinsa a zamansa na cibiyar kasuwanci a jihar Adamawa; cike da hada-hada har ma fiye da da; har yanzu garin na dauke da tabon abin firgitar da ya faru da shi shekaru bakwai baya; lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram suka fatattaki sojojin Najeriya tare da mamaye garin kuma suka rada masa suna Madinatul Islam.

Wakilin BBC da ya ziyarci birnin a tsakiyar wannan watan ya ga wasu gine-gine ciki har na bankuna wadanda mayakan suka lalata kuma har yanzu suke nan a rurrushe.

Kamar yadda har yanzu garin ke dauke da tabon wannan mamayar; haka zukatan mazaunansa.

''Gaskiya idan na tuna wannnan abin ko a mafarki ma yana ba ni tsoro. Muna jin (faduwar) bam, muna jin bam, muna jin bam." In Philip Tumba wani mazaunin garin.

"Da misalin karfe 10 na safe muka hau hanyar ficewa daga garin bayan a harsashe ya fada saman rufin da gidanda muke ciki." In shi.

Kodayake mafi rinjayen mazauna garin kamar su Mr. Tumba sun fice don tsoro abin ka iya faruwa da su a karkashin ikon ;yan Boko Haram; wasu tsoron ya hana su ficewa.

"Saboda muna tsoro ba mu je ko'ina ba. Muna ganin su ('yan Boko Haram) suna yawo cikin motoci ta ko'ina." Inji Musa Muhammad Biu wani dattijo a garin. Ya kara da cewa mayakan masu mamaya ba su yarda da kowa ba balle su zo kusa da kowa a lokacin har zuwa lokacin da suka fice.

Duk da cewa bayan 'yan makonni sojojin Najeriya sun sanar da sake ‚yanto garin; ga alamu abin firgitar da mazaunansa suka tarar bayan sun dawo ya ma fi na lokacin mamayar.

''Na dawo ranar 15 ga watan Disamba na tarar garin ba kowa. Na ga gawawwaki da kasusuwan mutane, a kofar gidanmu na a kofar gidanmu ma na samu kan mutum na dauke shi da itace na jefa a gota," inji Yakubu Tumba wani wanda 'ya'yansa 2 suka ɓata a lokacin yamutsin.

Duk da kasancewar yau shekaru bakwai da wannan mamayar dai; har yanzu abubuwan da suka biyo baya na matakan tsaro na ci gaba da tasiri a rayuwar jama'a.

Haramcin hawan babura da aka saka tun lokacin na nan daram. Baburan masu kafa uku suka maye gurbin baburan su ma dole ne su daina aiki bayan karfe bakwai na marece.

Masu tafiya a kasa da masu motocin hawa na da zuwa karfe goma- wani abu da ke sa farkon dare a garin yin tsit daren kuma yayi tsawo kamar daren yunwa.