Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Musa Baƙo
Sheikh Muhammad Musa Baƙo, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙungiyar Izalatul Bid'ah wa Iƙamatussunna ta jihar Borno ya ce soyayyarsa da ƙwallon ƙafa ta kusa shagaltar da shi a lokacin ƙuruciya.
Tarihin rayuwarsa
An haife shi a garin Dikwa kuma ya girma a ƙasar Chadi da Kamaru da Sudan inda lokacin da yake ƙarami iyayensa suka tafi da su a hanyarsu ta tafiya Saudiyya.
"Ina ƙanƙani ban ma san lokacin ba. Irin tafiyar nan ta da wadda ake yi in za a je Saudiyya. Sun tsaya a ƙasashe da ke kan hanyarsu, suka yi noma kafin suka wuce Saudiyya," a cewar Sheikh.
Ya ce sun daɗe a Chadi don har ya kai shekarun balaga ba su baro ƙasar ba.
Ya shaida wa BBC cewa a al'adar gidansu ba a yin karatun boko sai karatun tsangaya kuma shi ya yi a ɓangaren Al-Ƙur'ani da sauran littattafai.
An mayar da shi Maiduguri daga baya amma lokacin da aka fara yaƙi a Chadi sai iyayen nasa ma suka koma Najeriya.
Su waye malamansa?
Ya ce a malamansa na farko akwai Malam Siddik, sannan akwai Gwani Isa sai Malam Ɗayyabu wanda Allah Ya yi wa rasuwa da kuma Sheikh Muhammad Abba Aji.
"Ashheik Abubakar Garba Musa Ɗanyaya a wurinsa na yi karatun Mukhtasar," a cewar malam.
Ya bayyana cewa daga nan ne ya yi tunanin ya nemi ilimin boko duk da shekarunsa sun ɗan ja.
Ilimi
Sheikh Baƙo ya ce ya shiga makarantar Higher Islam ya fara tun daga ajin farko har ya gama.
"Mun zauna tare da ƴaƴan da ba su ma kai shekarun ƴaƴana ba amma na jure na gama a 1997. Daga nan kuma na shiga difloma duk a nan Higher Islam inda na karanci fannin shari'a kuma na kammala a 2003," in ji Malam.
Ya kuma bayyana cewa a shekarar 2010 ya shiga jami'ar Maiduguri inda a nan ya ɗan jima yana karanta fannin Larabci.
Ya bayyana cewa a lokacin da yake almajiri Suratul Nisa'i da Suratul Najm sun fi ba shi wahala.
"Suratul Nisa'i ta ba ni wahala saboda wajen rabon gadon nan lissafi ne. Ya ɗan ba ni wahala amma yanzu Alhamdulillahi," in ji shi.
Sheikh Baƙo ya ce babu surar da ya fi jin daɗin karantawa kamar Suratul Rahman, ya ce yana yawan maimaita wannan sura.
Ya ce littafin da ya fi son ya karantar shi ne tafsirin Al-Ƙur'ani.
Ya ce yana sha'awar karanta ayoyin Allah kuma ya karantar da su.
Me ya fi sa shi farin ciki?
Sheikh Baƙo ya ce babu abin da ya fi faranta masa rai irin matsayin da Allah Ya ba shi na almajiranci.
"Ba don komai ba sai don a iya tunanina babu wani matsayin da yake da farin ciki da alkhairi irin almajirci," a cewar malamin.
Yana son ya ci gaba da zuwa kamar Saudiyya don ya yi ibada kuma ya ziyarci kabarin Annabi tsira da aminci su tabbata a gareshi.
'Irin falala da ke cikin Sallah a Masallatan Makkah da Madina ya sa nake matuƙar ƙaunar zuwa Saudiyya. Ina so in gan ni ina Sallah a wadannan maslalatai, in sha ruwan zam-zam in yi safa da marwa," in ji Sheikh baƙo.
'Ina son cin tuwo'
Sheikh ya bayyana cewa yana son cin tuwo da miya.
"Ko wane irin gari ne ni dai na fi son in ci tuwo a kan ko wane abinci," in ji malamin.
Iyali
Malam yana da matan aure huɗu amma uwar gidansa ta rasu kwanan nan yanzu saura matansa uku.
Yana da ƴaƴa 28 kuma babban burinsa shi ne ya rayu yana wa'azi don tunatar da mai sauraro da kuma kansa.