Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Rudiger, Fulgini, Marcelo, Rice, Diaz, Perisic, da Pogba.

Asalin hoton, Getty Images
Everton da kuma West Ham suna cikin masu rubibin dan kwallon Inter Milan, Ivan Perisic ciki har da kungiyoyin da ke buga Bundesliga. (Fichajes - in Spanish)
Newcastle United sai ta tanadi kudi mai tsoka idan har tana son daukar kocin Ajax, Erik ten Hag domin maye gurbin Steve Bruce wanda ta kora. (Chronicle Live)
Kungiyoyin Premir League na son daukar dan wasan Angers, Angelo Fulgini tun bayan da dan wasan ya ci Paris St-Germain wata kayatacciyar kwallo a makon jiya. (Sun)
Dan kasar Brazil, Marcelo ya sanar da Real Madrid cewar yana son barin kungiyar a karshen kakar bana. Watakila kungiyar Brazil wato Fluminese zai koma da taka leda. (El Nacional - in Catalan)
Kocin West Ham, David Moyes ya ja kunnen duk kungiyar da ke son daukar Declan Rice ta tanadi fam miliyan 100. (Sky Sports via Manchester Evening News)
Chelsea ta yi bincike kan ko za a sayar mata da dan kwallon Porto, Luis Diaz sai dai Newcastle da Bayern Munich da kuma Real Madrid na son yin zawarcin dan kwallon. (Nicolo Schira on Twitter)
An dakatar da tattaunawa tsakanin Paul Pogba da Manchester United kan batun tsawaita zamansa a kungiyar sai cikin watan Afirilu za su ci gaba da batun in ji wakilansa Mino Raiola. (AS - in Spanish)
Mai tsaron baya Chelsea Antonio Rudiger zai iya barin kingiyar a karshen kakar badi, wanda ake alakanta shi da cewar zai koma taka leda a ko dai Juventus ko Manchester City ko Tottenham ko kuma Paris St-Germain. (Wettfreunde - in German)











