Man City za ta dauki Kross, Lingard zai koma Everton

Asalin hoton, EPA
Manchester United za ta yi dukkan abin da ya dace ta rike Paul Pogba, bayan da Real Madrid ke fatan daukar dan wasan idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar nan. (AS - in Spanish)
Kyaftin din Wolves, Conor Coady na cikin 'yan wasan da United ke son dauka a watan Janairu kan fam miliyan 20. (Sun)
Tsohon dan kwallon tawagar Netherlands, Marc Overmars ya fara tattaunawa da Newcastle domin karbar aikin daraktan kwallon kafar kungiyar. (Mirror)
Koci, Brendan Rodgers ya yi watsi da batun cewar dan kwallon Belgium, Youri Tielemans bai amince da yarjejeniyar da Leicester City ta gabatar masa ba, bayan da kungiyoyi da dama ke son yin zawarcinsa ciki har Liverpool da kuma Manchester United. (Mail)
Kungiyoyin Premier League na son zawarcin dan wasan FC Dallas Ricardo Pepi ciki har da Liverpool da kuma Manchester. (Mirror)
Dan wasan tawagar Argentina, Paulo Dybala, ya amince da sabuwar yarjejeniyar da Juventus ta gabatar masa kan ya ci gaba da taka leda a kungiyar. (Calciomercato - in Italian)
Kungiyar Sevilla ta ja kunnen Chelsea cewar ba za a sayar mata da mai tsaron baya, Jules Kounde, mai shekara 22 a arha ba. (Sun)
Kocin Manchester City, Pep Guardiola na son zawarcin dan wasan Real Madrid, Toni Kroos, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2023 a Sifaniya. (El Nacional - in Catalan)
Everton na kan gaba wajen rige-rigen sayen Jesse Lingard daga Manchester United, mai shekara 28 West Ham da kuma Newcastle na son daukar dan kwallon Ingilar. (Football Insider)
Dan kwallon tawagar Uruguay da Atletico Madrid, Luis Suarez na son ci gaba da taka leda a kungiyar da ke buga La Liga. Mai shekara 34 ya ci kwallo biyar a bana, wanda yarjejeniyarsa zai kare a karshen kakar badi. (Marca - in Spanish)
Ajax ba za ta bar Ryan Gravenberch ya koma wata kungiyar da taka led aba ta fara tattaunawa da shi kan tsawaita kwantiraginsa, bayan da Liverpool da Manchester United da Barcelona da kuma Juventus ke son daukar dan wasan. (Fichajes - in Spanish)









