Majalisar Wakilan Amurka ta samu abokin Trump da laifin kawo mata raini

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Wakilan Amurka ta yanke hukunci inda ta samu ɗaya daga cikin abokan tsohon Shugaban ƙasar Donald Trump da laifin raina majalisa sakamakon ƙin ba majalisar haɗin kai ya hallara a gabanta.
Tuni dai ƴan majalisar wakilan suka aika wa Steve Bannon goron gayyata domin ya hallara don amsa tambayoyi amma bai je ba.
Kwamitin da aka kafa domin ya binciki harin da aka kai wa majalisar Amurka a Janairun da ya wuce ne ya gayyaci Mista Bannon, sai dai wanda ake zargin ya kafe kai da fata cewa maganganun da suka tattauna da Mista Trump sirri ne kuma a bisa tsarin doka yana da kariya daga wani sashin ɓangaren zartarwa da ke kare maganganun da ya yi da tsohon shugaban.
A nasa ɓangaren, kwamitin da ke binciken ya ce Mista Bannon na da hujjojin da suke buƙata.
A yayin da yake magana kafin majalisar ta yanke hukuncin, Shugaban masu rinjaye a majalisar Steny Hoyer, ya ce akwai buƙatar a ɗauki mataki mai tsauri kan Mista Bannon.
"Ƙin zuwan da Mista Steve Bannon ya yi duk da gayyatar da muka yi masa a rubuce, alama ce a zahiri da ke nuna raininsa ba wai ga majalisar wakilai ba, amma ga kundin tsarin mulki da kuma dokar ƙasa baki ɗaya. Ba za a yarda da hakan ba kuma wannan mayar da hannun agogo baya ne a yunƙurin samun cikakken bayani kan abin da ya faru a ranar da aka kai hari a majalisa." in ji shi
Sai dai ƴan jam'iyyar Republican na zargin Democrats da ƙoƙarin saka son rai da nuna ɓangaranci da kuma saka siyasa ƙiriƙiri cikin wannan bincike.

Asalin hoton, Getty Images
Michelle Fischbach ƴar majalisar wakilai ce ƴar Jam'iyyar Republican masu adawa kuma cewa ta yi:
"Masu rinjaye na amfani da wannan kwamiti domin son ransu kuma a bayyane take cewa suna ƙoƙarin cimma manufar siyasa kan batun harin shida ga watan Janairu a maimakon su gudanar da bincike mai inganci kuma na tsakani da Allah kan gazawar da jami'an tsaro suka yi a wannan rana." in ji ta
A yanzu dai za a aika da wannan batun wajen ma'aikatar shari'ar Amurka da kuma Antoni Janar na ƙasar Merrick Garland domin yanke hukunci na ƙarshe kan ko a kama Mista Bannon da laifi.
Idan dai aka samu mutum da laifin raina majalisa a Amurka to akwai yiwuwar zai ɗanɗana kuɗarsa ta hanyan shafe shekara guda a gidan kaso da kuma biyan tarar dala dubu ɗari, sama da naira miliyan hamsin kenan.











