Ana zargin wasu ma'aurata da yunƙurin sayar da sirrukan nukuliyar Amurka

Asalin hoton, US Navy/Thiep Van Nguyen II
An kama wani Injiniyan rundunar sojin ruwan Amurka da mai ɗakinsa bisa zarginsu da yunƙurin sayar da sirrikan nukiliya ga wata ƙasa.
An kama Jonathan Toebbe da matar tasa Diana a West Virginia, kamar yadda ma'aikatar shari'a ta Amurkar ta sanar.
Ana zarginsu da ƙoƙarin sayar da taswiwar jigrin ruwa na ƙarƙashin teku mai amfani da makamashin nukiliya, inda suka ɓoye taswiwar a cikin wani ƙunshin biredi da aka shafe shi da man botar gyaɗa.
Sai dai a rashin sanunsu, wanda suka so su sayarwa wannan sirri, ma'aikacin hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ne.
Mista Toebbe ya yi aiki a ɓangaren gwajin makamin nukiliya na rundunar sojin ruwan Amurka kuma an amince masa sanin sirrika da kuma shiga duk wani lungu da saƙo.
Ma'aikatar shari'a ta ƙasar ta bayyana cewa a Afrilun 2020, wanda ake zargin ya tura da wani sunƙi zuwa ga wata ƙasa ɗauke da wasu bayanai muhimmai inda a ciki yake tallata cewa za su iya sayen wasu bayanan daga wurinsa.
Bayan haka ne ake zargin ya soma rubuta saƙon email da zaurance zuwa wani, inda a tunaninsa wanda yake aika wa saƙon yana wakiltar gwamnatin wata ƙasa ne, amma asali ma'aikacin FBI ne.
Bayan watanni da dama, sai Mista Toebbe da matarsa Diana suka yi wata yarjejeniya domin sayar da wasu bayanai kan dala 100,000 a kudin kirifto, kamar yadda ake zargi.
A watan Yunin bana sai suka kama hanya suka nufi West Virginia domin kai saƙon bayanan, inda a nan ne jami'an na FBI suka damƙe su.
A ranar Talata 12 ga watan Oktoban 2021 ne ake sa ran kotu za ta soma sauraren ƙarar waɗanda ake zargin da aka kai.














