Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sokoto: 'Ƴan bindiga sun kashe mutum 49 a kasuwar Goronyo'
Rahotanni daga jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya na cewa ƴan bidnga sun kashe aƙalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar.
Wasu ganau sun tabbatar wa da BBC labarin inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma, yayin da mutanen ke cin babbar kasuwar Goronyon.
Mutanen waɗanda suka buƙaci a sakaya sunayensu saboda tsaro sun ce ƴan bindigar sun afka wa kasuwar ne a yayin da ta cika makil da masu hada-hada daga sassan jihar da ma wasu yankunan.
"Ƴan fashin sun zo ne da misalin ƙarfe 4.30 zuwa biyar na yamma suka zagaye kasuwar suka buɗe wuta ta kowane ɓangare," in ji ganau ɗin.
BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ƴan sanda jihar, amma ba mu samu mai magana da yawun ƴan sanda ba a kiran waya da aka yi ta yi masa.
Kwamishinan tsaro na jihar ta Sakkwato Kanal Garba Moyi (ritaya) ya tabbatar da afkuwar lamarin, sai dai ya ce kawo lokacin da muka yi magana da shi ba a gama tattara alkalumman wadanda suka rasa rayukkan nasu ba.
Ganau ɗin ya ƙara da cewa "Mutane duk suka ruɗe wasu sun kwakkwanta a ƙasa don gudun harbin ya same su, yayin da wasu suka gudu amma masu tsautsayi sun rasa rayukansu."
Ganau ɗin sun ce an ƙidaya gawa 49 yayin da mutum 17 suka jikkata kuma tuni an kai su asibitin a birnin Sokoto, "gawarwakin kuma an kai mutuwaren da ke babban asibitin garin Goronyo," in ji ɗaya ganau ɗin.
Shaidun sun ce ƴan sandan kwantar da tarzoma da ƴan banga sun yi ƙoƙarin tarwatsa su amma ƴan fashin sun fi su yawa don haka suka kasa shawo kan lamarin.
"Daga baya jami'an tsaro sun je amma lokacin ƴan bindigar sun riga sun tafi," in ji shaidun.
Kowace Goronyo na ci ne a ranar kowace Lahadi, kuma mutane na zuwa daga faɗin jihar Sokoto da wasu jihohin har ma daga Jamhuriyyar Nijar.
Ƴan bindiga sun buɗe wuta ne a lokacin da mutane ke cin kasuwar garin Unguwar lalle, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.