An sako sarkin Bungudu da 'yan bindiga suka sace bayan ya shafe fiye da wata guda

Asalin hoton, Other
Rahotanni daga masarautar Bungudu a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an sako Sarkin Bungudu Alhaji Hassan Attahiru, da ƴan bindiga suka sace.
Babban dan sarkin Abdurrahman Hassan Attahiru, ya tabbatar wa BBC cewa an sako sarkin ne a daren Asabar 16 ga watan Oktoba bayan ya shafe kwanaki 32 a hannun 'yan bindiga.
Ya ce, an sako mahaifin na su a cikin koshin lafiya sai dai dan abin da ba a rasa ba saboda tsawon lokacin da ya kwashe a wajen 'yan bindigar.
Dan sarkin ya ce, kannan mahaifinsa da jami'an 'yan sanda da mambobin kungiyar Miyetti Allah da kuma gwamnatin jihar Zamfara ne suka karbo mahaifin na sa daga hannun wadanda suka sace shi.
Abdurrahman Hassan Attahiru, ya ce koda sukasamu labarin sako mahaifin na su sun yi farin ciki sosai wanda ba zai misaltu ba.
Ya ce, " Ba bu abin da zamu ce da jama'a ba na jihar Zamfara ba, duk wadanda suka ta ya mu addu'a a kan sako mahaifin mu sai godiya, haka gwamnatin jihar Zamfara ma mun gode mata dangane da tsayin da kan da ta yi wajen ganin an sako mahaifinmu''.
Ya ce, tun bayan da sarkin ya dawo gida bai ce musu komai ba a game da yanayin da ya kasance a lokacin da ya ke hannun 'yan bindigar.
Kuma batun koan bada kudin fansa wajen sako mahaifinmu ni ban sani ba saboda ban san komai ba a kai don kannan mahaifinmu ne a kan komai tun bayan da aka sace shi, in ji dan sarkin.
A ranar 14 ga watan Satumbar, 2021, ne aka sace sarkin Sarkin mai daraja ta ɗaya a jihar Zamfara, a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja daga Kaduna.
Akwai ɗan sanda ɗaya da aka kashe lokacin da ƴan bindigar suka yi awon gaba da sarkin.
Ba wannan ne karon farko ba da ake samun rahotannin sace sanannun sarakuna a arewacin Najeriya, amma wannan ne karon farko da aka sace Sarki mai daraja ta daya dakuma ya shafe fiye da wata guda a hannun 'yan bindiga kafin sako shi.











