Hotunan Afirka na mako 8-14 Oktoba 2021: Masu sintiri a gabar teku da magoya bayan ƙwallo

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna na ƴan Afirka da kuma na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

Short presentational grey line
Diana Kipyogei of Kenya wears a gilded crown.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An bai wa Diana Kipyogei ɗan Kenya kambu bayan yin nasara a Gasar Tsere ta Boston ranar Litinin.
A mural depicting Archbishop Desmond Tutu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne aka sake dawo da wannan zanen fentin na Archbishop Desmond Tutu, wanda ya cika shekara 90 a makon da ya gabata a birnin Cape Town, bayan da a baya masu wariyar launin fata suka goge shi.
A woman wears South African football colours and the national flag.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan mai goyon bayan ƙwallon ƙafar na nuna goyon bayanta ga Afirka Ta Kudu a wasan neman shiga gasar ƙwallon kafar dunuya da aka yi a Habasha ranar Talata, inda kungiyar Bafana Bafana ta ci 1-0.
A plaque in Bamum script.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan hoton an manna shi ne a jikin kofar shiga Fadar Masarautar Foumban a yammacin Kamaru...
People of Bamoun prepare the throne of Mfonrifum Nabil Mbombo Njoya .

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Litinin ne aka nada Mfonrifum Nabil Mbombo Njoya mai shekara 28 a matsayin sabon sarki wato Sultan na Bamoun.
Spectators watch a competitor drive over a dune on a motorbike.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mutane na kallin tseren babura a cikin hamada a yankin Merzouga ranar Lahadi.
An activist waves the LGBTQ flag outside the court.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu fafutuka a ranar Talata sun taru don sauraron shari'a a wata babbar kotu a Botswana, inda gwamnati take so a sauya hukuncin da aka yanke na halasta luwadi.
Personal effects of parishioners and deacons killed at Chena Teklehaymanot Church in Chena, Ethiopia.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Lahadi, kwana 40 bayan kisan kiyashin da aka yi a Cocin Chena Teklehaymanot a yankin Amhara na Habasha, ana iya ganin kayayyakin mutanen da suka mutu a kan taga. Jami'an Amhara sun ce dakarun Tigray za a zarga, su kuma sun yi watsi da zargin.
An aerial view of elephants living in Amboseli National Park.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani garken giwaye na wucewa a cikin Gandun Daji na Amboseli na, wajen da ake samun ƙaruwar haihuwar giwaye.
Somali marine forces patrol the Indian Ocean.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jamia'n sojin ruwan Somaliya suna sintiri a bakin gabar tekun kasar ranar Laraba, sakamakon shari'ar da aka yanke kan rikicin kan iyaka tsakanin Kenya da Somalia wacce ta yi wa Somaliyan dadi.
A police helicopter is seen flying over police officials wearing face masks.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Taron tsuntsaye na shawago a sararin samaniya a daidai lokacin da wani helikwafta ke a sa shawagin a Tripoli babban birnin Libiya ranar Asabar.
People fly kites at the Dolphin Beach in Cape Town, South Africa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Washe gari a Afirka ta Kudu mutane na jefa jiragen leda a sararin sama.
A man washing a puppy in the sea.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, A ranar Alhamis a Mauritius, wani mutum ya yi wa karensa wanka a gabar Tekun Indiya.

All pictures subject to copyright.