Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fu Zhenghua: An tsare tsohon ministan shari'ar China
Hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a China na binciken tsohon ministan shari'a kuma shugaban hukumar kare jama'ar ƙasar.
A farkon shekarar nan ne aka cire Mista Fu Zhenghua daga muƙaminsa na minista. Wata sanarwa da aka fitar ta ce an tsare shi kuma ana bincikar shi ne bisa zargin saɓa ƙa'idoji.
Mista Zhenghua ne jami'in ƙasar na baya-bayan nan da aka sa gaba a yaƙin da ƙasar ke yi da cin hanci da rashawa.
Sama da shekara takwas kenan tun bayan da Shugaban China Xi Jinping ya fara mulkar ƙasar inda kuma ya lashi takobin saka kafar wando ɗaya da duk wani jami'in ƙasar babba ko ƙarami da aka zarga da cin hanci.
Sai dai a yanzu ana neman kakkaɓo babban jami'in da ake ganin ya kai ƙololuwa a harkokin gudanarwa a Chinar.
A matsayinsa na shugaban ƴan sandan Beijing, Fu Zhenghua ya samu karɓuwa a lokacin da ya yi dirar mikiya kan lauyoyi masu bore da kuma masu fafutikar kare haƙƙin bil adama.
Mista Zhenghua ya miƙa a aikin nasa inda ya riƙe manyan muƙamai a babban birnin ƙasar - ciki har da ministan shari'a da kuma shugaban hukumar kare jama'ar ƙasar.
Ya mayar da hankalinsa wajen daƙile irin cin hancin da ake yi a sashen ƴan sanda haka kuma ya yi maganin sanannun masu rubuce-rubuce a intanet.
Haka kuma ya jagoranci wani babban bincike da ya yi sanadiyyar gano cewa tsohon shugaban tsaro na China Zhou Yongkang na da hannu dumu-dumu a badaƙalar cin hanci da rashawa, inda yanzu haka yake zaman ɗaurin rai da rai a gidan yari.
Haka kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen binciken Ling Jihua, wani tsohon mai bai wa shugaban ƙasar Hu Jintao shawara inda shi ma aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Sai dai ana ganin binciken irin waɗannan manyan zakunan da suka yi ƙarfi a gwamnati abu ne mai matuƙar haɗari, wanda hakan ya sa masu sharhi game da gwamnatin Shugaba Xi Jingpin ke ganin yaƙin da yake yi da cin hanci wata hanya ce ta kawar da maƙiyansa.
A bara ne dai aka sanar da ritayar Fu Zhenghua daga aiki, amma a yanzu ya shiga cikin dubban jami'an gwamnatin China da ake farautarsu bisa zargin cin hanci.