R Kelly: An samu mawaƙin da laifin cin zarafin mata da ƙananan yara

Asalin hoton, Getty Images
An samu mawakin nan na Amurka R Kelly, da laifin amfani da matsayinsa na fitaccen tauraro wajen shirya makarkashiyar lalata mata da kananan yara a tsawon shekara ashirin.
Mutum goma sha daya da suka zarge shi, mata tara da maza biyu, sun ba da bahasi daya bayan daya a shari'a mai zafi da aka shafe mako shida ana gudanarwa inda suka bayyana irin cin zarafin da suka fuskanta a hannunsa.
Bayan sun shafe kwana biyu suna nazari a kan zargin, masu taya alkali yanke hukunci sun samu R Kelly da laifi a kan dukkan zarge-zargen da aka yi masa.
A ranar 4 ga watan Mayun shekara mai zuwa ne za a yanke masa hukuncin wanda ake sa ran zai shafe aƙalla shekara 15 a gidan yari.
Masu taya alkali shari'ar, sun samu R Kelly da laifin kasancewa jagoran wani shiri wanda ake jawo hankalin mata da kananan yara a yi amfani da su ta hanyar lalata.
Mawakin wanda ya yi fice tare da karbar lambar yabo bayan ya yi wakarsa ta I Believe I Can Fly -, an same shi da laifin safarar mata tsakanin jihohin Amurka, tare da shirya fina-finan batsa na yara.
Daya daga cikin matan wadda ta bayar da shaidar cewa Kelly, ya bata kwaya ta sha sannan ya mata fyade, ta ce ta jima tana boye wa Kelly saboda barazanar da ya rinka yi mata tun bayan da ta furta maganar a bainar jama'a.
Ta ce," A shirye na ke na fara rayuwata kamar kowa na fitar da tsoron da ke tattare da ni, sannan na fara murmurewa daga abin da ya faru da ni".
Takardun shari'ar sun bayyana irin gallazawar da R Kelly ya rinka yi wa mutanen, inda ba a barinsu cin abinci ko amfani da bandaki ba tare da izininsa ba.
Haka kuma shi ke iko da kayan da suke sanyawa, sannan kuma ya sa suna kiransa da suna "Daddy".
Gloria Allred, lauya ce da ke wakiltar da yawa daga cikin wadanda abin ya shafa, ta shaida wa manema labarai cewa, ta shafe shekara 47 tana aikin shari'a, ta sha kuma cin karo da laifukan cin zarafi kala-kala, amma ba ta taba haduwa da mafi muni kamar na Mr Kelly ba.
Hukuncin ya zo shekara 13 bayan an wanke R Kelly, daga tuhume-tuhumen shirya fina-finan batsa ga yara a wata shari'a da aka yi a jihar Illinois.
Yawancin zarge-zargen da aka saurara a shari'ar an fara bankada su ne a wasu shirye-shirye masu dogon zango da aka yi wa taken Surviving R Kelly, a 2019.
Yawancin wadanda abin ya shafa an zabe su ne daga cikin masu zuwa kallon wakarsa, ko kuma wadanda aka ce za a taimaka musu su zama mawaka.












