Ayyukan da za mu yi idan mun ciyo bashin naira biliyan 100 - Gwamnan Adamawa

An wallafa

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan shirin gwamnatin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na karbo rancen naira biliyan 100.

Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya ce za a yi amfani da kudin ne wajen gyara kasuwannin dabbobi da kuma hatsi don inganta samun kudin shiga a jihar.

To amma ita kuwa jam'iyar APC mai adawa ta ce dabara ce ta wawure kudin al'umma.

A wata hira da BBC, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya ce ya zama dole a samo sabbin hanyoyin samun kudin shiga domin rage dogaro kan gwamnatin tarayya da kuma kudin mai.

Tun a lokacin da gwamnan ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta karbi rancen a watan Mayu ne aka fara tayar da jijiyoyin wuya tsakanin bangaren gwamnati da na 'yan adawa a jihar.

Gwamnati na cewa wata sabuwar hanya ce ta samun kudin shiga ta gano domin rage dogaro kan gwamnatin tarayya, su kuwa 'yan adawa cewa suke yi wata hanya ce ta yin sama da fadi da kudaden al'umma.

Gwamna Fintiri ya ce 'yan adawa ne ba su fahimci yadda abin yake ba.

"Mutane ne wadanda ba su gane yadda tsarin yake ba suka dauko maganar suna ta surutu, maganar bashi babu ita.

"Idan kuma an dauki bashi bisa wannan tsarin, tsarin ne zai haifar da kudi da za a biya wannan bashin da shi, don haka babu laifi" a cewar gwamna Fintiri.

"A yanzu wa zai ba ka kudi cikin duhun kai? Bari in gaya maka, duk sa daya da ya bar Mubi yaje jihar Lagos ya hau kan kwata, aka yanka, dubu goma Lagos ke karba, saboda haka a shekara daya jihar tana samun biliyan 27 daga shanu da ke shiga cikinta daga garin Mubi da ke jihar Adamawa.

"Gaya mini idan muka fara wannnan harkar a Adamawa muka samu wadannan kudaden asara muka yi?"

Gwamnan ya kara da cewa fa'idar da shirin rancen ke da shi ne yasa a taron gwamnonin yankin Arewa maso gabashin Najeriya da ya gudana kwanakin baya a Jalingo fadar jihar Taraba, gwamnonin suka bukaci dukkan jihohinsu su kaddamar da irin shirin.

Abin da 'yan adawa ke cewa

Tun bayan sanar da batun karbo rancen jam'iyar adawa ta APC a jihar ta fito ta yi fatali da shi.

APC na ganin gwamnati na yunkurin wawure kudaden da ta ce za ta karbo ne.

Mukaddashin sakataren jam'iyar a Adamawa Mr. Wafari Theman ya ce wannan ba shi ne lokacin da ya fi dacewa a karbo rance ba ganin cewa ta kashe kudade sama da naira biliyan takwas wajen gina gadar sama.

"Yaya gwamnati za ta binne biliyan-biliyan a cikin siminti wanda ba ya kawo amfani sannan kuma ta ce za ta je kasuwa ta karbi rance a kan riba don inganta noma, me ya sa ba ta yi amfani da kudin da aka binne wajen yin noma ba tuntuni?'

'Su waye ne wadanda za su yarda su zuba jarin? Wa ka ga ya shigo ya ce zai saya? Me suka gani a kasa? Ai akwai hatsari a cikin wannan abun," in ji Mr. Wafari.

Su ma al'ummar jihar ra'ayoyin su ya kasu kashi uku kan wannan batun, a yayin da wasu ke ganin abu ne da zai taimaka mata ta farfado wasu kuwa na ganin ba lallai ne ayi amfani da kudaden ta yadda ya dace ba, sai kuma 'yan tsaka-tsaki masu jiran ganin yadda shirin zai kaya.

Gwamnati dai ta daurawa cibiyar Arewa Research and Development Project alhakin aiwatar da shirin gaba dayan shi.

Shugaban cibiyar Aminu Buhari ya ce za a samo kudin ne daga hannun masu zuba jari karkashin jagorancin FBM Quest kuma za a yi amfani da kudin ne wajen inganta kasuwannin sayar da dabbobi da hatsi a jihar.

A halin yanzu al'ummar jihar Adamawa na jiran ganin yadda wannan rancen zai habaka kudin shiga da jihar ke samu daga naira biliyantakwas zuwa naira biliyan 45 a shekara ta 10 bayan karbo rancen da ake sa ran zai inganta kasuwannin dabbobi da kuma hatsi dake garuruwan Mubi da Ganye da Ngurure da Cigari da kuma sauransu.