An cimma matsaya tsakanin China da Amurka kan Huawei

Meng Wanzhou (a tsakiya) tana barin kotun Koli ta British Columbia

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Meng Wanzhou (a tsakiya) tana barin kotun Koli ta British Columbia
An wallafa

An kawo karshen takaddamar diflomasiyya tsakanin China da Amurka da Canada, inda aka saki babbar jami'ar kudi ta kamfanin Huawei na China, wadda aka tsare a Canada.

Tuni dai Meng Wanzhou ta tashi zuwa China haka su ma wasu 'yan Canada biyu da China ta tsare Michael Kovrig da Michael Spavor an sake su, inda suka shiga jirgin sama domin komawa Canada.

An dai saki Ms Meng wadda aka kama tun 2018 daga daurin talala a gida karkashin wata yarjejeniya da masu gabatar da kara na Amurka, wadanda tun da farko suka bukaci tasa keyarta zuwa Amurkar, inda tsarewar tata ta janyo rikicin diflomasiyya.

Ana ganin Meng Wanzhouta bar filin jirgin sama na Vancouver a wannan jirgin na China zuwa Shenzhen

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana ganin Meng Wanzhouta bar filin jirgin sama na Vancouver a wannan jirgin na China zuwa Shenzhen

An nuna Ms Meng Wanzhou ne inda ta bayyana ta bidiyo a wata kotu a birnin New York tana musantawa ko kin amsa tarin laifukan almundahana na banki da ake mata.

Wanda wannan shi ne karshe ko kololuwar yarjejeninyar da aka cimma da ma'aikatar shari'a ta Amurka, wadda ta bayar da damar barin jami'ar barin Canada inda ake tsare da ita a gida tun 2018.

Sai dai a wani bangare na yarjejeniyar sakin nata babbar jami'ar kudin ta kamfanin na Huawei ta yarda cewa ta yi wa bankuna karya domin taimaka wa kamfanin saba takunkumin tattalin arziki da Amurka ta sanya wa Iran

Batun nata ya zama wata alama da ke nuni da irin tsattsamar dangantakar da ke tsakanin kasashen duniya biyu mafiya karfi, China da Amurka.

Ita ma dai Canada an shigar da ita rikicin, inda China ta mayar da martini ta hanyar tsare 'yan kasarta biyu.

Huawei

Asalin hoton, Getty Images

Yarjejeniyar shari'ar wadda aka dage ta wanke Meng Wanzhou, wadda diya ce ga wanda ya kafa kamfanin na Huawei.

Amma kuma har yanzu katafaren kamfanin sadarwar na China n fuskantar tuhuma a Amurka wadda ta hada da ta liken asiri.

Kuma har yanzu ba a sani ba ko idan wannan maslaha da aka yi za ta taimaka wa 'yan Canadan biyu. Har kullum China na musanta cewa abubuwan biyu suna da alaka.