Tsarin fensho na PENCOM na cutar da mu in ji 'yan sandan Najeriya

An wallafa

Wasu tsoffin 'yan sandan da ke kan tsarin fensho na PENCOM a Najeriya, sun yi kira ga mahukunta da su cire su daga tsarin da suka ce yana cutar da su.

A bisa wannan dalili, wasu daga cikin irin waɗannan 'yan sanda da suka yi ritaya sai da suka yi zanga-zanga don jawo hankalin hukumomi a kan bambancin da suka ce ana nuna musu wajen samun haƙƙoƙinsu, duk da yake sun shafe shekara-da-shekaru suna bautawa ƙasa.

Tsoffin 'yan sandan sun ce ba a biyansu cikakken hakkinsu na fensho duk kuwa da shekarun da suka shafe suna aikin tsaron kasa.

A jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, wasu daga cikin tsoffin 'yan sandan sun gudanar da zanga-zangar lumana inda suka je shalkawatar 'yan sandan jihar a wani mataki na nuna rashin jin dadinsu a game da yadda ake biyansu hakkokinsu.

CSP John Madaki, mai ritaya na daya daga cikin 'yan sandan da suka yi wannan zanga-zanga, ya kuma shaida wa BBC cewa, tsarin da ake bi wajen biyansu kudaden fansho tamkar kisan mummuke ake musu a fakaice.

Ya ce,"An zo an ce wai an samu a wani tsari wai shi ',PENCON' to mu a gaskiya bamu gane ba, domin idan kayi riyata kudin daya kamata a biya ka ba a baka duka, sai a raba maka".

Ya ce, sun yi rubuce-rubuce kala-kala, amma bata sauya zani ba.

To sai dai mahukunta a harkar fenshon 'yan sandan kasar ta Najeriya sun ce suna sane da matsalar, har ma sun kai batun gaba.