Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afghanistan: Taliban ta hana mata komawa aiki a Kabul
Mutumin da ke rike da mukamin Magajin garin Kabul na rikon kwarya da Taliban ta nada ya gaya wa mata ma'aikata na birnin da su zauna a gida, sai dai kawai wadanda maza ba za su iya maye gurbin ayyukansu ba ne kawai za su je aiki.
Hamdullah Nomani, ya ce sun dauki wannan mataki ne saboda ya zama dole su dakatar da mata daga aiki na wani dan lokaci.
Wannan shi ne mataki na baya-bayan nan da kungiyar mai tsattsauran ra'ayi ta dauka a kan mata.
Magajin garin ya ce kashi daya cikin uku na ma'aiktan hukumar kwaryar birnin na Kabul su kusan dubu uku mata ne.
Ya ce wasu daga cikin mata ma'aikatan misali masu gyara bandakin mata, da wadanda ke aikin zayyana da masu aikin injiniya za su iya ci gaba da zuwa wuraren aikinsu.
Amma wadanda maza za su iya yin aikinsu, ya ce sun gaya musu su zauna a gida har sai al'amura sun koma daidai, amma ya ce za a ci gaba da biyansu albashinsu.
Ranar Lahadi da ta gabata wasu mata sun dan yi zanga-zanga a wajen ma'aikatar kula da harkokin matan, yayin da wasu tarin matan kuma suka yi wani taron manema labarai inda suke bukatar 'yancinsu.
Daya daga cikin matan da ke zanga-zangar ta ce ba sa son a kawar da wannan ma'aikata, domin cire mata na nufin cire dan adam.
Yayin da ake wannan kuma hukumar tabbatar da 'yancin dan adam mai zaman kanta ta Afganistan ta ce ba ta iya gudanar da ayyukanta ba tun bayan da Taliban ta kwace iko.
Kungiyar ta ce a wata sanarwa, gine-ginenta da motocinta da kwanfutocinta duk 'yan Taliban sun kame suna aiki da su.
Wasu daga cikin ma'aikatan gwamnatin Afghanistan din mata sun koka da matakin suna cewa su ne ke daukar dawainiyar iyalansu saboda haka ya kamata a kyale su su koma bakin aikinsu
A zamanin mulkin Taliban din na farko a shekarun 1990, sun hana mata aiki da kuma hana 'yan mata zuwa makaranta.
Kungiyar ta Taliban ga alama ta rufe tsohuwar ma'aikatar kula da harkokin matan.
Domin an ga an maye allo da sauran alamu da ke wajen ma'aikatar harkokin matan, aka maye su da wasu na ma'aikatar wanzar da kyawawan dabi'u da yaki da alfasha.
A zamanin mulkin kungiyar na shekarun 1990, ma'aikatar ita ce ta 'yan Hisbah wato 'yan sandan tabbatar da ɗa'a ga dokokin addinin Islama.
Jami'an da ake tsoronsu a kan yadda aka ce ba sa saurara wa mata su sake da kuma yadda suke tilasta bin fahimtarsu ta dokokin Shari'ar Musulunci.
Bayan da suka kwace mulkin kasar ta Afghanistan a watan da ya wuce, sakamakon janyewar sojojin Amurka, Taliban din ta ce za ta mutunta hakkin mata, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A karshen makon nan da ya gabata sun sake bude makarantun sakandire, amma kuma dalibai maza da malamai maza kawai suka ba dama su ci gaba da karatu.
Amma kuma sun ce suna aiki kan yadda za a sake bude makarantun mata.