Afghanistan: Ɗalibai maza sun koma makaranta a ƙasar ban da mata

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Taliban ta ware mata daga karatun boko a Afghanistan inda a sabuwar sanarwar da ta fitar ta amince ɗalibai maza da malamansu maza su koma azuzuwa domin ci gaba da karatu.
Wasu dalibai mata a ƙasar sun shaida wa BBC cewa ransu ya ɓaci sakamakon hana su komawa makaranta.
Jami'an Taliban, waɗanda suka ƙwace iko da Afghanistan a watan da ya gabata sun ce suna ta ƙoƙarin cimma matsaya kan wannan lamari.
Mutane da dama na cikin fargaba inda suke shakkar dawowar irin mulkin Taliban na shekarun 1990 a inda suka rinƙa take haƙƙin mata a ƙasar.
A ƙarƙashin sabuwar gwamnatin, jami'an Taliban sun bayyana cewa za a bar mata su yi karatu ne bisa tsarin da suka ce addinin Musulunci ya shimfiɗa.
Sai dai mata masu zuwa aiki a halin yanzu an ce su zauna a gida har sai an samu sauƙi ta ɓangaren matsalar tsaro da ake fama da ita, haka kuma rahotanni na cewa mayaƙan Taliban ɗin sun rinƙa dukan mata waɗanda suka fita zanga-zanga inda suke adawa da yadda maza suka yi ka-ka gida a gwamnatin.
A ranar Juma'a Taliban ɗin ta rufe ma'aikatar harkokin mata inda ta maye gurbin ma'aikatar da sashen da ke tabbatar da an aiwatar da sharuɗɗan da addini ya gindaya.
'Na damu kan makomar rayuwata a nan gaba'
Wata sanarwa da aka fitar kafin bude makarantun a ranar Asabar ta ce: "Duka malamai da ɗalibai maza su koma makarantunsu."
Masu zuwa makarantar sakandire akasarinsu suna tsakanin shekara 13 ne zuwa 18 kuma yawancinsu ana nuna musu wariya.
Sai dai daga baya kamfanin dillancin labarai na Bakhtar a ƙasar ya ruwaito mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid na cewa ba da daɗewa ba za a buɗe makarantun mata.
Kakakin ya kuma bayyana cewa jami'an Taliban ɗin na ƙoƙarin warware batun jigila ga ɗaliban makaranta da suka ɗan tasa.
Ɗalibai mata da iyayensu a ranar Asabar sun bayyana cewa suna cikin damuwa kan makomarsu.
"Na damu matuƙa kan rayuwata a nan gaba," in ji wata ɗaliba a Afghanistan wadda ke da burin zama lauya.
"Yanzu kam muna cikin duhu. Duk safiya idan na tashi bacci ina tambayar kaina me ya sa har yanzu nake raye? Ko dai na zauna gida ne na jira wani ya ƙwanƙwasa ƙofa ya tambaye ni na aure shi? Wannan shi ne kawai amfanin mace?"
Mahaifinta ya bayyana cewa : "Mahaifiyata ba ta yi karatu ba kuma mahaifina ya rinƙa zaluntarta da kuma zaginta. Ba na son ƴata ta zama kamar mahaifiyata."
Wata ɗalibar ƴar shekara 16 daga Kabul ta bayyana cewa wannan rana ce ta"baƙin ciki".
"Na so na zama likita! sai dai wannan burin ya tafi. Ba na tunanin za su bari mu koma makaranta. Ko da sun sake buɗe makarantu, ba su son a ilmantar da mata."
A farkon makon nan ne Taliban ɗin ta sanar da cewa za a bar mata su yi karatu a jami'o'i sai dai ba za a bari su cakuɗu da maza ba haka kuma za a fitar musu da sabon tsarin saka tufafi.
Wasu sun bayyana cewa waɗannan sabbin dokokin za su hana mata karatu sakamakon jami'o'i ba su da ƙarfin da za su samar da azuzuwa na daban ga mata.
Haka kuma hana matan zuwa makarantun sakandire na nufin ba macen da za a bari ta ci gaba da karatunta.

Tun bayan da aka hamɓarar da gwamnatin Taliban a 2001, an samu ci gaba matuƙa a ɓangaren ilimi a Afghanistan musamman ga mata.
Yawan matan da ake da su a makarantun firamare ya ƙaru daga 0 zuwa miliyan 2.5, inda adadin matan da ke karatu ya ruɓanya cikin shekara 10 da kashi 30. Sai dai akasarin ci gaban an fi samunsa a birane.
"Wannan koma baya ne a ɓangaren ilimin ƴaƴa mata a Afghanistan," in ji Nororya Nizhat, tsohuwar mai magana da yawun ma'aikatar ilimi ta ƙasar."
Jim kaɗan bayan kwace mulkin ƙasar, Taliban ta bayyana cewa za ta mutunta haƙƙoƙin mata da shari'ar Musulunci ta shimfiɗa.











